Search engine for discovering works of Art, research articles, and books related to Art and Culture
ShareThis
Javascript must be enabled to continue!

Kwatance a Waƙoƙin Makaɗan Sitidiyo: Tsokaci Daga Wasu Waƙoƙin Sarauta na Haruna Aliyu Ningi

View through CrossRef
Wannan takarda ta yi nazarin salon Kwatance ne a wasu waƙoƙin sarauta na Haruna Aliyu Ningi. A cikin takardar an fito da misalai na kwatantawa tare da yi musu sharhi. An ɗora nazarin wannan takarda bisa Mazhabar Nazarin Waƙar Baka Bahaushiya ta Gusau (2015). Dabaru da hanyoyin da aka bi wajen gudanar da wannan takarda sun haɗa da hira da Haruna Aliyu Ningi da wasu manazarta waƙar baka. Sannan an samo waƙoƙin ne kai tsaye daga wurin Haruna Ningi a inda aka juye su a rubuce domin samun saƙin nazari. Binciken ya gano Haruna Aliyu Ningi yana amfani da dabarar adonta harshe ta kwatantawa waɗanda suka haɗa da kamantawa ta daidaito da ta fifiko da siffantawa da jinsintarwa wanda ta haɗa da abuntarwa da mutuntarwa da dabbantarwa da kuma alamtarwa.Gudummawar da takardar za ta bayar ita ce ƙara ba da haske ga manazarta da ɗalibai ta yadda za su nazarci adon harshe a waƙoƙin baka na Hausa.
Title: Kwatance a Waƙoƙin Makaɗan Sitidiyo: Tsokaci Daga Wasu Waƙoƙin Sarauta na Haruna Aliyu Ningi
Description:
Wannan takarda ta yi nazarin salon Kwatance ne a wasu waƙoƙin sarauta na Haruna Aliyu Ningi.
A cikin takardar an fito da misalai na kwatantawa tare da yi musu sharhi.
An ɗora nazarin wannan takarda bisa Mazhabar Nazarin Waƙar Baka Bahaushiya ta Gusau (2015).
Dabaru da hanyoyin da aka bi wajen gudanar da wannan takarda sun haɗa da hira da Haruna Aliyu Ningi da wasu manazarta waƙar baka.
Sannan an samo waƙoƙin ne kai tsaye daga wurin Haruna Ningi a inda aka juye su a rubuce domin samun saƙin nazari.
Binciken ya gano Haruna Aliyu Ningi yana amfani da dabarar adonta harshe ta kwatantawa waɗanda suka haɗa da kamantawa ta daidaito da ta fifiko da siffantawa da jinsintarwa wanda ta haɗa da abuntarwa da mutuntarwa da dabbantarwa da kuma alamtarwa.
Gudummawar da takardar za ta bayar ita ce ƙara ba da haske ga manazarta da ɗalibai ta yadda za su nazarci adon harshe a waƙoƙin baka na Hausa.

Related Results

Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin dangantakar ‘yantauri da sarauta da masaurata a wasu waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsarin zaman...
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Gurbin Waƙoƙin Yara Mata da ‘Yammata a Rayuwar Hausawa
Gurbin Waƙoƙin Yara Mata da ‘Yammata a Rayuwar Hausawa
Waƙoƙin yara mata da ‘yammata wani babban rukuni ne a al’adar Hausawa. Waƙoƙi ne da ake yi domin samun nishaɗi da tarbiyya da ilmantarwa da kuma gargaɗi ga ‘yammata tun suna ƙanana...
Dabarun Jawo Hankali a Waƙar ‘Yandotan Tsahe Alhaji Aliyu Ta Alhaji Musa Ɗankwairo Maradun
Dabarun Jawo Hankali a Waƙar ‘Yandotan Tsahe Alhaji Aliyu Ta Alhaji Musa Ɗankwairo Maradun
Makaɗan baka na Hausa sun karkasu dangane da rukunan mutanen da suke yi wa kiɗa da waƙa. Waɗannan rabe-rabe na makaɗan baka sun haɗa da makaɗan fada-wato waɗanda suke yi wa fadar s...
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin dangantakar mata da maza, wato ‘yantauri da mafarauta da makamantansu a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsari...
Turken Nasaba a Cikin Wasu Waƙoƙin Abdun Inka Bakura
Turken Nasaba a Cikin Wasu Waƙoƙin Abdun Inka Bakura
Waƙa wata fasaha ce da Allah ya hore wa ɗan’Adam wajen amfani da harshensa da tunaninsa, domin ya isar da saƙo ga al’ummar da yake a cikinsu. Allah ya albarkaci ƙasar Hausa da nau’...
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
A adabin baka na Hausawa, waƙa tana ɗaya daga cikin manyan hanyoyin isar da saƙo da hikima. Waƙar baka na da salo da fasaha iri-iri, ciki har da ɓoyayyen saƙo. Ɗaya daga cikin salo...
Turken Zuga da Yabo a Zubin Wasu Ɗiyan Waƙoƙin Alhaji Sa’idu Faru: Nazari DagaWaƙar Turakin Kano Alhaji Ahmadu
Turken Zuga da Yabo a Zubin Wasu Ɗiyan Waƙoƙin Alhaji Sa’idu Faru: Nazari DagaWaƙar Turakin Kano Alhaji Ahmadu
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin turken zuga da yabo a waƙar Turakin Kano. Don haka zuga ko yabo ɗaya ne daga cikin turakun waƙoƙin makaɗan baka na Hausa, musam...

Back to Top