Search engine for discovering works of Art, research articles, and books related to Art and Culture
ShareThis
Javascript must be enabled to continue!

Karin Magana a Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai

View through CrossRef
Sunan wannan maƙala shi ne karin magana a cikin waƙoƙin Alhaji Musa Danba'u Gidan Buwai. Manufar maƙala ita ce nazari da sharhi kan yadda Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai yake sarrafa karin magana a cikin wakokinsa don a fito da baiwa da hikimomi da zalaƙar harshe da Allah ya ba shi wadda yake amfani da su wajen shirya waƙoƙinsa. An bi hanyoyi guda biyu wajen binciken, wato yin hira da iyalansa da abokan hulɗarsa musamman waɗanda suke taimaka masa wajen gudanar da sana’arsa ta waƙa, da kuma nazarin waƙoƙin. An dora aikin ne bisa ga littafin Farfesa Sa'idu Muhammad Gusau mai taken Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Bayan nazarin waƙoƙin. Sakamakon ya nuna akwai karin magana a cikin waƙoƙin nasa.
Title: Karin Magana a Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai
Description:
Sunan wannan maƙala shi ne karin magana a cikin waƙoƙin Alhaji Musa Danba'u Gidan Buwai.
Manufar maƙala ita ce nazari da sharhi kan yadda Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai yake sarrafa karin magana a cikin wakokinsa don a fito da baiwa da hikimomi da zalaƙar harshe da Allah ya ba shi wadda yake amfani da su wajen shirya waƙoƙinsa.
An bi hanyoyi guda biyu wajen binciken, wato yin hira da iyalansa da abokan hulɗarsa musamman waɗanda suke taimaka masa wajen gudanar da sana’arsa ta waƙa, da kuma nazarin waƙoƙin.
An dora aikin ne bisa ga littafin Farfesa Sa'idu Muhammad Gusau mai taken Jagoran Nazarin Waƙar Baka.
Bayan nazarin waƙoƙin.
Sakamakon ya nuna akwai karin magana a cikin waƙoƙin nasa.

Related Results

Zambo A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u
Zambo A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u
A kowane lokaci adabin al’uma kan fayyace yadda rayuwa da tsarin zamantakewar al’umar ke wakana ne, ta yadda ake sa rai idan an dubi adabin wannnan al’umar a iya hango hoton rayuwa...
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
An rubuta maƙalar domin a fito da salon hira da ke cikin waƙoƙin da aka ambata a sama domin tabbatar da akwai shi a cikin waƙoƙin da ake magana a kai. Salon hira na nufin tattaunaw...
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Gurbin Waƙoƙin Yara Mata da ‘Yammata a Rayuwar Hausawa
Gurbin Waƙoƙin Yara Mata da ‘Yammata a Rayuwar Hausawa
Waƙoƙin yara mata da ‘yammata wani babban rukuni ne a al’adar Hausawa. Waƙoƙi ne da ake yi domin samun nishaɗi da tarbiyya da ilmantarwa da kuma gargaɗi ga ‘yammata tun suna ƙanana...
Danganatakar Karin Magana Da Tunanin Bahaushe: Tsokaci Daga Magana Jari Ce Na Abubakar Imam
Danganatakar Karin Magana Da Tunanin Bahaushe: Tsokaci Daga Magana Jari Ce Na Abubakar Imam
Ilimin hikimomin al’umma fage ne da ake nazarin tarihin tsofaffin kayan kimiyyar al’umma masu alaƙa da cigaban ɗanadam. ilimin hikimomin al’umma ya ƙunshi rassa da dama da suka haɗ...
Turken Nasaba a Cikin Wasu Waƙoƙin Abdun Inka Bakura
Turken Nasaba a Cikin Wasu Waƙoƙin Abdun Inka Bakura
Waƙa wata fasaha ce da Allah ya hore wa ɗan’Adam wajen amfani da harshensa da tunaninsa, domin ya isar da saƙo ga al’ummar da yake a cikinsu. Allah ya albarkaci ƙasar Hausa da nau’...
Tubalin Yabon Mata a Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo
Tubalin Yabon Mata a Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da matsayin mata a wasu waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo ta sigar yabo. Dalilin da ya sa mutane ba su yi rubutu sosai ba, saboda hankali bai ...
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin dangantakar ‘yantauri da sarauta da masaurata a wasu waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsarin zaman...

Back to Top