Search engine for discovering works of Art, research articles, and books related to Art and Culture
ShareThis
Javascript must be enabled to continue!

Aron Kalmomi Daga Wasu Sassan Harsuna: Nazarin Hausar ‘Yan-tashar Mota a Garin Sakkwato

View through CrossRef
Manufar wannan takardar ita ce, a aiwatar da nazarin kalmomin aro a Hausar ‘yan-tashar mota a garin Sakkwato. Haka kuma, takardar ta yi amfani da ra’in da ya shafi yadda mutane suke amfani da harshe ta fuskar ma’anar kalmomi, wato Ra’in Fiɗar Zantuttuka (Discourse Analysis Theory)’ wanda Harris (1952) ya assasa. Sannan, an yi amfani da hanyoyi biyu wajen tattara bayanai waxanda suka haxa da tattaunawa da kuma lura ta kai-tsaye. Takardar ta gano ‘yan-tashar mota a garin Sakkwato suna sarrafa kalmomin aro wajen ambaton direbobi da yaran mota da ‘yan kamasho da ‘yan dako da fasinja da tashar mota da motoci da jami’an tsaro, ko kuma don su bayyana wani hali da suka tsinci kan su a cikin tasha ko a halin tafiya.
Title: Aron Kalmomi Daga Wasu Sassan Harsuna: Nazarin Hausar ‘Yan-tashar Mota a Garin Sakkwato
Description:
Manufar wannan takardar ita ce, a aiwatar da nazarin kalmomin aro a Hausar ‘yan-tashar mota a garin Sakkwato.
Haka kuma, takardar ta yi amfani da ra’in da ya shafi yadda mutane suke amfani da harshe ta fuskar ma’anar kalmomi, wato Ra’in Fiɗar Zantuttuka (Discourse Analysis Theory)’ wanda Harris (1952) ya assasa.
Sannan, an yi amfani da hanyoyi biyu wajen tattara bayanai waxanda suka haxa da tattaunawa da kuma lura ta kai-tsaye.
Takardar ta gano ‘yan-tashar mota a garin Sakkwato suna sarrafa kalmomin aro wajen ambaton direbobi da yaran mota da ‘yan kamasho da ‘yan dako da fasinja da tashar mota da motoci da jami’an tsaro, ko kuma don su bayyana wani hali da suka tsinci kan su a cikin tasha ko a halin tafiya.

Related Results

Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Kwatancin Halayen Masu Nakasar Kisan-Raɓa Tsakanin Al’umma Da ‘Yan Taurin Kassu Zurmi
Kwatancin Halayen Masu Nakasar Kisan-Raɓa Tsakanin Al’umma Da ‘Yan Taurin Kassu Zurmi
Duk da cewar waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi sun fi mayar da hankali a kan rukunin maza (‘yan tauri); hakan bai hana a iya ƙyllaro hoton wasu mutane a cikinsu ba. Wannan takarda ta dubi...
Nazarin Rikiɗar Wasu Sautukan Harshen Ngizim Zuwa Hausa
Nazarin Rikiɗar Wasu Sautukan Harshen Ngizim Zuwa Hausa
A duk lokacin da aka samu wata cuɗanya ta mu’amala tsakanin harsuna mabambanta guda biyu, akan samu harshe mafi tasiri a tsakaninsu. Irin wannan dangantaka ta tsakanin harsuna, ita...
Salo a Littafin Amon ‘Yanci na Halima Ahmad Matazu
Salo a Littafin Amon ‘Yanci na Halima Ahmad Matazu
Fagen nazarin salo, fage ne mai faxi wanda yake da buqatar a ci gaba da nazarta domin fito da hikimomi da zalaqar harshe da Allah ya albarkaci fasihai da marubuta na Hausa. Duk da ...
Faɗi-Tashin Auren Bahaushe:Nazari daga waƙar kassu zurmi ta shayi ɗangidan labbo
Faɗi-Tashin Auren Bahaushe:Nazari daga waƙar kassu zurmi ta shayi ɗangidan labbo
A kowane lokaci, mai neman nazarin wani abu na al’ada idan ya ratsi waƙoƙin baka na Hausa, yakan ji shi warkal irin na wanda ya shiga rijiya da dawonsa. Buƙatar wannan nazari ne ya...
Nazarin Aikatau a Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Aikatau a Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Wannan takarda mai taken “Nazarin Aikatau a Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi” ta yi sharhin aikatau dangane da abin da ya shafi giredi, musamman dangane da Hausar Yamma. Harshen Hau...
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
A adabin baka na Hausawa, waƙa tana ɗaya daga cikin manyan hanyoyin isar da saƙo da hikima. Waƙar baka na da salo da fasaha iri-iri, ciki har da ɓoyayyen saƙo. Ɗaya daga cikin salo...
Nazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu Waƙoƙin Siyasa na Hausa
Nazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu Waƙoƙin Siyasa na Hausa
Wannan takarda mai takenNazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu waƙoƙin siyasa na Hausa,n rubuta ta ne da niyyar fito da ire-iren hikimomi da basirar da mawallafan siyasa suke amfani da ...

Back to Top