Search engine for discovering works of Art, research articles, and books related to Art and Culture
ShareThis
Javascript must be enabled to continue!

Tasirin Mawaƙan Baka Wajen Haɓaka Al-Adun Hausawa

View through CrossRef
Ƙasar Hausa kamar yadda tarihinta ya zo a litattafai da dama, suna alaƙanta ta da mazaunin Hausawa na farko kafin su watsu zuwa sassa daban-daban na duniya. Mu’azu (1993:1) ya bayyana ainihin ƙasar Hausa ta asali da “tana Afirka ta yamma ne, a farfajiyar da ke tsakanin hamadar sahara da kuma dazuzzukan da suka doshi gaɓar tekun atlantika, watau daga kudu. Kuma ana kiran ƙasar da sunan Sudan ta yamma, watau tafkin Chadi da kuma gwiwar kogin Kwara a can yamma.” A wani ƙaulin kuwa Dokaji, (1978) ya bayyana ƙasar Hausa da ƙasa ce da ta daɗe da wanzuwa a yammacin afirka wadda kuma ba a iya haƙiƙance lokacin fara wanzuwarta. A cewar wasu masana, ƙasar Hausa ita ce yankin nan na ƙasar Sudan wanda ke wajen tsakiya- tsakiya. Daga gabas da ita akwai ƙasar Borno, daga yamma ƙasar Dahomey (wacce yanzu ake kira jamhuriyar Benin), daga arewa hamadar sahara, daga kudu kuma ƙasashen da ake kira “Middlebelt”. Alhasan, (1982) Ya ce, asalin ƙasar Hausa ya faro ne daga ƙauyukan Lalle da Asodu da ke arewa maso gabas da Agadas can cikin ƙasar Nijar. Daga can Gobirawa suka taso kaɗan-kaɗan suka taru a muhallinsu na yanzu da ke cikin arewacin Nijeriya.
Title: Tasirin Mawaƙan Baka Wajen Haɓaka Al-Adun Hausawa
Description:
Ƙasar Hausa kamar yadda tarihinta ya zo a litattafai da dama, suna alaƙanta ta da mazaunin Hausawa na farko kafin su watsu zuwa sassa daban-daban na duniya.
Mu’azu (1993:1) ya bayyana ainihin ƙasar Hausa ta asali da “tana Afirka ta yamma ne, a farfajiyar da ke tsakanin hamadar sahara da kuma dazuzzukan da suka doshi gaɓar tekun atlantika, watau daga kudu.
Kuma ana kiran ƙasar da sunan Sudan ta yamma, watau tafkin Chadi da kuma gwiwar kogin Kwara a can yamma.
” A wani ƙaulin kuwa Dokaji, (1978) ya bayyana ƙasar Hausa da ƙasa ce da ta daɗe da wanzuwa a yammacin afirka wadda kuma ba a iya haƙiƙance lokacin fara wanzuwarta.
A cewar wasu masana, ƙasar Hausa ita ce yankin nan na ƙasar Sudan wanda ke wajen tsakiya- tsakiya.
Daga gabas da ita akwai ƙasar Borno, daga yamma ƙasar Dahomey (wacce yanzu ake kira jamhuriyar Benin), daga arewa hamadar sahara, daga kudu kuma ƙasashen da ake kira “Middlebelt”.
Alhasan, (1982) Ya ce, asalin ƙasar Hausa ya faro ne daga ƙauyukan Lalle da Asodu da ke arewa maso gabas da Agadas can cikin ƙasar Nijar.
Daga can Gobirawa suka taso kaɗan-kaɗan suka taru a muhallinsu na yanzu da ke cikin arewacin Nijeriya.

Related Results

Izga Da Matsayinta a Bahaushiyar Al’ada
Izga Da Matsayinta a Bahaushiyar Al’ada
Munafar wannan takarda ita ce fito da amfanin izga a tunanin Hausawa a wajen amfani na yau da kullum da kuma wajen magance wasu cututtuka, musamman a mahangar ‘yanbori. Haka kuma, ...
Tarbiya a Falsafar Al’ada
Tarbiya a Falsafar Al’ada
Al’ummar Hausawa sun daɗe suna gudanar da harkokin rayuwarsu kamar yadda al’adarsu ta tanada. Kowace al’umma haka ake sa ran takasance tana alfahari da al’adunta. Tarbiya tana daga...
Sunayen Hausawa na Gargajiya a Cikin Waƙoƙin Abubakar Kassu Zurmi
Sunayen Hausawa na Gargajiya a Cikin Waƙoƙin Abubakar Kassu Zurmi
Duk wani abu da ya shafi fasahar bayyana nagartaccen tsarin rayuwa ta mutum da kuma al’umma wadda ta shafi duniya da wadda ta shafi Lahira tana nan tule a cikin waƙoƙin baka na Hau...
Gurbin Sana’o’in Gargajiyar Hausawa a Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Gurbin Sana’o’in Gargajiyar Hausawa a Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Babbar manufar maƙalar ita ce fito da sana’o’in gargajiya na Hausawa, waɗanda Kassu Zurmi ya taskace a cikin waƙoƙinsa tare da duban yadda shi makaɗin ya kalle su a cikin waƙoƙinsa...
Faɗi-Tashin Auren Bahaushe:Nazari daga waƙar kassu zurmi ta shayi ɗangidan labbo
Faɗi-Tashin Auren Bahaushe:Nazari daga waƙar kassu zurmi ta shayi ɗangidan labbo
A kowane lokaci, mai neman nazarin wani abu na al’ada idan ya ratsi waƙoƙin baka na Hausa, yakan ji shi warkal irin na wanda ya shiga rijiya da dawonsa. Buƙatar wannan nazari ne ya...
Salon Sakaɗe a Waƙoƙin Baka na Hausa: Duba Cikin Wasu Shahararrun Waƙoƙin Mashahuran Mawaƙan Baka
Salon Sakaɗe a Waƙoƙin Baka na Hausa: Duba Cikin Wasu Shahararrun Waƙoƙin Mashahuran Mawaƙan Baka
Burin wannan bincike lalubo wani salo daga cikin salailai da mawaƙan baka ke amfani da su wajen isar da saƙonsu ga masu sauraron su. An yi wa binciken take “Salon Sakaɗe: an ƙago s...
Makaɗan Hausa A Gombe: Tasirin Makaɗan Fada A Masarautar Buba Yero
Makaɗan Hausa A Gombe: Tasirin Makaɗan Fada A Masarautar Buba Yero
Hausawa mutane ne da aka san su da shiga lungu-lungu da saƙo-saƙo na yankunan maƙwabtansu na kusa da na nesa. Mutane ne da ke da sha’awar tafiye-tafiye don neman kyakkyawar matsugu...
Nazarin Koɗawa da Washi a Zubin Ɗiyan Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Koɗawa da Washi a Zubin Ɗiyan Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Manufar wannan takarda [1] ita ce a aiwatar da nazari kan wasu waƙoƙin Kassu Zurmi yadda yake amfani da tubalin koɗawa da washi wajen gina gundarin saƙo a zubin ɗiyan waƙoƙinsa. An...

Back to Top