Search engine for discovering works of Art, research articles, and books related to Art and Culture
ShareThis
Javascript must be enabled to continue!

Makaɗan Hausa A Gombe: Tasirin Makaɗan Fada A Masarautar Buba Yero

View through CrossRef
Hausawa mutane ne da aka san su da shiga lungu-lungu da saƙo-saƙo na yankunan maƙwabtansu na kusa da na nesa. Mutane ne da ke da sha’awar tafiye-tafiye don neman kyakkyawar matsuguni na samun ɗan abin tasarrufi na sa wa a bakin salati. A duk inda suka ya da zango sukan yi wa al’ummar da suka taras tasiri da harshensu da al’adunsu. Wannan takarda ta yi nazarin makaɗa da mawaƙan fada waɗanda suka kwararo jihar Gombe kuma suke rayuwa suna nishaxantar da masarautar ta Fulani da kaɗe-kadensu da waƙoƙinsu na fasaha da bushe-bushensu. An kuma kawo dalilai da suka haifar da zuwan Huasawa ƙasar Gombe da sabubban cuɗanyarsu da Fulani a Gombe. Takardar ta yi amfani da hanyar hira da masu ba da bayanai da kuma ajiyayyun takardu don tattara bayanai da suka taimaka wajen taskace nau’o’in makaɗa da mawaƙan Hausa da suke masarautar. Daga ciki, an kawo makaɗan taushi da na turu da na kotso da na ganga da na ruwa da kuma masu bushe-bushe. An yi bayanin waɗanda suka assasa kowane kiɗa a masarautar da inda suka fito da waɗanda suka gaje su, da kuma lokutan da suka fi gabatar da waƙoƙin nasu. Binciken ya gano akwai makaɗan Hausa maza da mata a fadar masarautar da suka shafi dukkan rukuni na mawaƙan da aka gabatar a nan sama. An kuma kawo ‘yan misalai na wasu ɗiyan waƙoƙin makaɗan. Binciken ya nuna yadda ‘ya’ya da jikoki da aka haifa a masarautar suka taimaka wajen gina al’ummar nan da aka fi sani da Hausa/Fulani wato narkewar al’adun al’ummu guda biyu waje ɗaya.
Title: Makaɗan Hausa A Gombe: Tasirin Makaɗan Fada A Masarautar Buba Yero
Description:
Hausawa mutane ne da aka san su da shiga lungu-lungu da saƙo-saƙo na yankunan maƙwabtansu na kusa da na nesa.
Mutane ne da ke da sha’awar tafiye-tafiye don neman kyakkyawar matsuguni na samun ɗan abin tasarrufi na sa wa a bakin salati.
A duk inda suka ya da zango sukan yi wa al’ummar da suka taras tasiri da harshensu da al’adunsu.
Wannan takarda ta yi nazarin makaɗa da mawaƙan fada waɗanda suka kwararo jihar Gombe kuma suke rayuwa suna nishaxantar da masarautar ta Fulani da kaɗe-kadensu da waƙoƙinsu na fasaha da bushe-bushensu.
An kuma kawo dalilai da suka haifar da zuwan Huasawa ƙasar Gombe da sabubban cuɗanyarsu da Fulani a Gombe.
Takardar ta yi amfani da hanyar hira da masu ba da bayanai da kuma ajiyayyun takardu don tattara bayanai da suka taimaka wajen taskace nau’o’in makaɗa da mawaƙan Hausa da suke masarautar.
Daga ciki, an kawo makaɗan taushi da na turu da na kotso da na ganga da na ruwa da kuma masu bushe-bushe.
An yi bayanin waɗanda suka assasa kowane kiɗa a masarautar da inda suka fito da waɗanda suka gaje su, da kuma lokutan da suka fi gabatar da waƙoƙin nasu.
Binciken ya gano akwai makaɗan Hausa maza da mata a fadar masarautar da suka shafi dukkan rukuni na mawaƙan da aka gabatar a nan sama.
An kuma kawo ‘yan misalai na wasu ɗiyan waƙoƙin makaɗan.
Binciken ya nuna yadda ‘ya’ya da jikoki da aka haifa a masarautar suka taimaka wajen gina al’ummar nan da aka fi sani da Hausa/Fulani wato narkewar al’adun al’ummu guda biyu waje ɗaya.

Related Results

Dabarun Jawo Hankali a Waƙar ‘Yandotan Tsahe Alhaji Aliyu Ta Alhaji Musa Ɗankwairo Maradun
Dabarun Jawo Hankali a Waƙar ‘Yandotan Tsahe Alhaji Aliyu Ta Alhaji Musa Ɗankwairo Maradun
Makaɗan baka na Hausa sun karkasu dangane da rukunan mutanen da suke yi wa kiɗa da waƙa. Waɗannan rabe-rabe na makaɗan baka sun haɗa da makaɗan fada-wato waɗanda suke yi wa fadar s...
Hausa
Hausa
With an estimated population of up to 50 million, Hausa make up one of the largest people groups practicing Islam. Despite settlement of today’s Hausaland in the central Sudan by t...
Hausa
Hausa
The term “Hausa” refers to a language spoken by over thirty million first-language speakers living mainly in the region now comprising northern Nigeria and southern Niger, with lar...
Sociolinguistic aspects of the spoken version of Hausa in Ghana
Sociolinguistic aspects of the spoken version of Hausa in Ghana
Even though Hausa is not an indigenous Ghanaian language but it plays a very important role in Ghana’s sociolinguistics. It is the lingual franca for many people living in the zong...
Hausa Political Music and Political Engagements on Social Media during Nigeria’s 2023 General Elections
Hausa Political Music and Political Engagements on Social Media during Nigeria’s 2023 General Elections
The use of Hausa political music has become a key feature during electioneering campaigns in northern parts of Nigeria. This paper examines how Hausa political music were used for...
Nazarin Tsarin Sauti a Hausar Yamma
Nazarin Tsarin Sauti a Hausar Yamma
Dialectology is an area of linguistics that is concerned with the studies of similarities and differences in speech forms of a particular language. Dialectologists are more interes...
Waziri Tijjani and His Contributions for the Spread and Development of Tijjaniyya Sufi Order in Nigeria
Waziri Tijjani and His Contributions for the Spread and Development of Tijjaniyya Sufi Order in Nigeria
Islam as a practical religion on earth has penetrated almost all corners of the world. Tijjaniyyah also contributed for dissemination and the spread of Islam in Gombe. This researc...

Back to Top