Javascript must be enabled to continue!
Al’adun Hausawa a Duniyar Intanet: A San Matsayin Yau Don a Kyautata Gobe
View through CrossRef
Manufar wannan maƙala ita ce nazartar al’adun Hausawa a duniyar intanet ta yau. An ɗora aikin a kan Bahaushen ra’i na Zamani Riga. Kadadar binciken ta taƙaita ga al’adun Hausawa da duniyar intanet. Tussan bayanai na farko da aka yi amfani da su sun kasance kafafen intaent kai tsaye. Majiya ta biyu kuwa ta kasance ayyukan da suka gabata waɗanda suke da alaƙa da wannan bincike. Sakamakon binciken ya nuna cewa, tuni Hausa ta kama hanyar samun gagarumin gindin zama a duniyar intanet. Al’adun Hausawa daban-daban na bayyana yayin da aka neme su ta hanyar injunan biɗar bayanai na kan intanet. Ƙalubalen da ake fuskanta a wannan haujin sun haɗa da ƙarancin masana masu jagorantar lamuran kafafen intanet na Hausa, da kuma rashin ingancin bayanan da ake ɗorawa a kan kafafen. Daga ƙarshe, binciken ya nuna wajibcin ƙara himma ga masana da manazarta harshe da adabi da kuma al’adun Hausawa wajen sanya rigar zamani da samar da kyakkyawan wakilci a duniyar intanet.
SASPR Edu International Pvt. Ltd
Title: Al’adun Hausawa a Duniyar Intanet: A San Matsayin Yau Don a Kyautata Gobe
Description:
Manufar wannan maƙala ita ce nazartar al’adun Hausawa a duniyar intanet ta yau.
An ɗora aikin a kan Bahaushen ra’i na Zamani Riga.
Kadadar binciken ta taƙaita ga al’adun Hausawa da duniyar intanet.
Tussan bayanai na farko da aka yi amfani da su sun kasance kafafen intaent kai tsaye.
Majiya ta biyu kuwa ta kasance ayyukan da suka gabata waɗanda suke da alaƙa da wannan bincike.
Sakamakon binciken ya nuna cewa, tuni Hausa ta kama hanyar samun gagarumin gindin zama a duniyar intanet.
Al’adun Hausawa daban-daban na bayyana yayin da aka neme su ta hanyar injunan biɗar bayanai na kan intanet.
Ƙalubalen da ake fuskanta a wannan haujin sun haɗa da ƙarancin masana masu jagorantar lamuran kafafen intanet na Hausa, da kuma rashin ingancin bayanan da ake ɗorawa a kan kafafen.
Daga ƙarshe, binciken ya nuna wajibcin ƙara himma ga masana da manazarta harshe da adabi da kuma al’adun Hausawa wajen sanya rigar zamani da samar da kyakkyawan wakilci a duniyar intanet.
Related Results
Nason Wasu Al’adun Kyautata Zamantakewar Hausawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nason Wasu Al’adun Kyautata Zamantakewar Hausawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Al’adun kyautata zamantakewa, al’adu ne masu ɗimbin yawa da har yau ba a ƙayyade su ba, da ma dai al’ada ita ce sababbiyar hanyar gudanar da rayuwa. Don haka dukkan tsarin da al’ad...
Tarbiya a Falsafar Al’ada
Tarbiya a Falsafar Al’ada
Al’ummar Hausawa sun daɗe suna gudanar da harkokin rayuwarsu kamar yadda al’adarsu ta tanada. Kowace al’umma haka ake sa ran takasance tana alfahari da al’adunta. Tarbiya tana daga...
On the Convergence Analysis of Yau–Yau Nonlinear Filtering Algorithm: From a Probabilistic Perspective
On the Convergence Analysis of Yau–Yau Nonlinear Filtering Algorithm: From a Probabilistic Perspective
Abstract.
At the beginning of this century, a real time solution of the nonlinear filtering problem without memory was proposed in [S.-T. Yau and S. S.-T. Yau, Ma...
Basira Da Aiki Da Basira a Harshen Mata Hausawa
Basira Da Aiki Da Basira a Harshen Mata Hausawa
Takarda ce da aka yi yunƙuri domin ankarar da yadda ake amfani da basira a cikin zantukan mata Hausawa. Nazarin ya tabbatar da cewa mata na da basira da aiki da basira a cikin zant...
Sunayen Hausawa na Gargajiya a Cikin Waƙoƙin Abubakar Kassu Zurmi
Sunayen Hausawa na Gargajiya a Cikin Waƙoƙin Abubakar Kassu Zurmi
Duk wani abu da ya shafi fasahar bayyana nagartaccen tsarin rayuwa ta mutum da kuma al’umma wadda ta shafi duniya da wadda ta shafi Lahira tana nan tule a cikin waƙoƙin baka na Hau...
On pre-Calabi-Yau categories
On pre-Calabi-Yau categories
Sur les catégories de pre-Calabi-Yau
Dans cette thèse, nous étudions les catégories de pré-Calabi-Yau et leurs morphismes.Nous développons pour cela un outil nous p...
Izga Da Matsayinta a Bahaushiyar Al’ada
Izga Da Matsayinta a Bahaushiyar Al’ada
Munafar wannan takarda ita ce fito da amfanin izga a tunanin Hausawa a wajen amfani na yau da kullum da kuma wajen magance wasu cututtuka, musamman a mahangar ‘yanbori. Haka kuma, ...
Nau’o’in Abincin Hausawa a Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nau’o’in Abincin Hausawa a Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Wannan maƙala ta bibiyi wasu waƙoƙin Abubakar Kassu Zurmi, domin fito da nau’o’in abincin Hausawa na gargajiya da suke ƙunshe a ciki. Haka kuma, maƙalar ta kafa hujja da waɗansu ɗi...

