Search engine for discovering works of Art, research articles, and books related to Art and Culture
ShareThis
Javascript must be enabled to continue!

Basira Da Aiki Da Basira a Harshen Mata Hausawa

View through CrossRef
Takarda ce da aka yi yunƙuri domin ankarar da yadda ake amfani da basira a cikin zantukan mata Hausawa. Nazarin ya tabbatar da cewa mata na da basira da aiki da basira a cikin zantukansu na yau da kullum. Sakamakon Takardar ta gano tun tan gini tun rane, mata Hausawa na amfani da basira da aiki da basira tun fil azal, amma yau da gobe al’amuran zalaƙa da fasaha da hikima na ƙara bunƙasa kamar yadda binciken ya gano ya ba da misalai. Haka kuma mata na da rukunoni da dama waɗanda suke bayyanar da basirar amfani da harshe kamar yadda maƙalar ta gano. Manufar wannan maƙala ita ce ta fito da waɗannan bayanai a fili domin amfanin masana da manazarta harshen Hausa, musamman ta fuskar walwalar harshe. An yi amfani da ra’in siffantawa (Descriptive Theory) domin yi bayyanin wannan maƙala, kasancewar duk wani aiki da ya shafi nazarin walwalar harshe a kan sami nasarar bincike, in an ɗora shi a kan wannan ra’i. Haka kuma an yi amfani da littafai da maƙaloli da masana da manzarta suka rubuta wajen waiwayan aikin da suka gabata. Sannan an saurari maganganun mata Hausawa a matsayin masu ruwa da tsaki. A ƙarshe ana fatan wannan aiki ya zama mai amfani ga manazarta walwalan ilimin harshe.
Title: Basira Da Aiki Da Basira a Harshen Mata Hausawa
Description:
Takarda ce da aka yi yunƙuri domin ankarar da yadda ake amfani da basira a cikin zantukan mata Hausawa.
Nazarin ya tabbatar da cewa mata na da basira da aiki da basira a cikin zantukansu na yau da kullum.
Sakamakon Takardar ta gano tun tan gini tun rane, mata Hausawa na amfani da basira da aiki da basira tun fil azal, amma yau da gobe al’amuran zalaƙa da fasaha da hikima na ƙara bunƙasa kamar yadda binciken ya gano ya ba da misalai.
Haka kuma mata na da rukunoni da dama waɗanda suke bayyanar da basirar amfani da harshe kamar yadda maƙalar ta gano.
Manufar wannan maƙala ita ce ta fito da waɗannan bayanai a fili domin amfanin masana da manazarta harshen Hausa, musamman ta fuskar walwalar harshe.
An yi amfani da ra’in siffantawa (Descriptive Theory) domin yi bayyanin wannan maƙala, kasancewar duk wani aiki da ya shafi nazarin walwalar harshe a kan sami nasarar bincike, in an ɗora shi a kan wannan ra’i.
Haka kuma an yi amfani da littafai da maƙaloli da masana da manzarta suka rubuta wajen waiwayan aikin da suka gabata.
Sannan an saurari maganganun mata Hausawa a matsayin masu ruwa da tsaki.
A ƙarshe ana fatan wannan aiki ya zama mai amfani ga manazarta walwalan ilimin harshe.

Related Results

Tasirin Karin Harshen Zamfarci a Fassarar Keɓaɓɓun Kalmomin Kiwon Lafiya a Asibitin Ƙwararru Ta Yariman Bakura
Tasirin Karin Harshen Zamfarci a Fassarar Keɓaɓɓun Kalmomin Kiwon Lafiya a Asibitin Ƙwararru Ta Yariman Bakura
Karin harshe yana taka muhimmiyar rawa wajen samar da ingantacciyar sadarwa kamar yadda fassara ke da matuƙar muhimmnci a ɓangaren kiwon lafiya, musamman a karkara da ƙauyuka.Wani ...
Sunayen Hausawa na Gargajiya a Cikin Waƙoƙin Abubakar Kassu Zurmi
Sunayen Hausawa na Gargajiya a Cikin Waƙoƙin Abubakar Kassu Zurmi
Duk wani abu da ya shafi fasahar bayyana nagartaccen tsarin rayuwa ta mutum da kuma al’umma wadda ta shafi duniya da wadda ta shafi Lahira tana nan tule a cikin waƙoƙin baka na Hau...
Nazarin Rikiɗar Wasu Sautukan Harshen Ngizim Zuwa Hausa
Nazarin Rikiɗar Wasu Sautukan Harshen Ngizim Zuwa Hausa
A duk lokacin da aka samu wata cuɗanya ta mu’amala tsakanin harsuna mabambanta guda biyu, akan samu harshe mafi tasiri a tsakaninsu. Irin wannan dangantaka ta tsakanin harsuna, ita...
PENGAPLIKASIAN KERAJINAN MATA-MATA PADA BUSANA DENGAN TEKNIK PRINTING
PENGAPLIKASIAN KERAJINAN MATA-MATA PADA BUSANA DENGAN TEKNIK PRINTING
Kerajinan mata-mata merupakan ciri khas dari daerah Simeulue yang memiliki ragam motif yang unik dan warna yang khas. Namun keragaman motif, keunikan serta kekhasan dari motif  mat...
Tarbiya a Falsafar Al’ada
Tarbiya a Falsafar Al’ada
Al’ummar Hausawa sun daɗe suna gudanar da harkokin rayuwarsu kamar yadda al’adarsu ta tanada. Kowace al’umma haka ake sa ran takasance tana alfahari da al’adunta. Tarbiya tana daga...
Nau’o’in Abincin Hausawa a Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nau’o’in Abincin Hausawa a Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Wannan maƙala ta bibiyi wasu waƙoƙin Abubakar Kassu Zurmi, domin fito da nau’o’in abincin Hausawa na gargajiya da suke ƙunshe a ciki. Haka kuma, maƙalar ta kafa hujja da waɗansu ɗi...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...

Back to Top