Search engine for discovering works of Art, research articles, and books related to Art and Culture
ShareThis
Javascript must be enabled to continue!

Turken Zuga da Yabo a Zubin Wasu Ɗiyan Waƙoƙin Alhaji Sa’idu Faru: Nazari DagaWaƙar Turakin Kano Alhaji Ahmadu

View through CrossRef
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin turken zuga da yabo a waƙar Turakin Kano. Don haka zuga ko yabo ɗaya ne daga cikin turakun waƙoƙin makaɗan baka na Hausa, musamman ma, makaɗan fada. Ra’in da aka yi amfani da shi wajen ɗora wannan bincike, an gudanar da shi bisa kwatance kawai, an yi ƙoƙarin fito da ɗiyan waƙoƙin da suka dace da binciken ne, sannan aka yi sharhi a kansu ta yadda za fito da ma’anar da suke ɗauke da ita, wadda ta dace da binciken. Wannan bincike an gudanar da shi ta hanyar nazarta waƙoƙin Alhaji Sa’idu Faru waɗanda aka rubuta su a wasu littattafai da kundayen bincike da aka gabatar a matakai daban-daban, sai dai binciken ya taƙaita ne ga waƙa guda ɗaya ta Alhaji Ahmadu Turakin Kano. A wajen kawo ɗiyan waƙar da aka yi magana a kan su, an cire gindin waƙar sannan aka yi sharhi kan manufar gindin waƙar. Dukkanin ɗiyoyin da aka kawo an juya su ne kamar yadda aka rubuta su a littattafan da aka yi nazari a cikinsu. Takardar ta gano Alhaji Sa’idu Faru yakan yabi duk wani wanda ya yi masa alkhairi ko aka yi masa alkhairi saboda shi. Haka kuma an gano irin zuga da yake yi wa wanda ya zaɓi ya yi masa waƙa, yakan nuna hazaƙarsa da bajintarsa da fasaharsa wajen kwarzanta da zuga duk abin da ya so ya yi wa waƙa. Takardar ta yi ƙoƙarin sharhanta wasu daga cikin ɗiyan da ya bayyana zuga da yabo a cikinsu.
Title: Turken Zuga da Yabo a Zubin Wasu Ɗiyan Waƙoƙin Alhaji Sa’idu Faru: Nazari DagaWaƙar Turakin Kano Alhaji Ahmadu
Description:
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin turken zuga da yabo a waƙar Turakin Kano.
Don haka zuga ko yabo ɗaya ne daga cikin turakun waƙoƙin makaɗan baka na Hausa, musamman ma, makaɗan fada.
Ra’in da aka yi amfani da shi wajen ɗora wannan bincike, an gudanar da shi bisa kwatance kawai, an yi ƙoƙarin fito da ɗiyan waƙoƙin da suka dace da binciken ne, sannan aka yi sharhi a kansu ta yadda za fito da ma’anar da suke ɗauke da ita, wadda ta dace da binciken.
Wannan bincike an gudanar da shi ta hanyar nazarta waƙoƙin Alhaji Sa’idu Faru waɗanda aka rubuta su a wasu littattafai da kundayen bincike da aka gabatar a matakai daban-daban, sai dai binciken ya taƙaita ne ga waƙa guda ɗaya ta Alhaji Ahmadu Turakin Kano.
A wajen kawo ɗiyan waƙar da aka yi magana a kan su, an cire gindin waƙar sannan aka yi sharhi kan manufar gindin waƙar.
Dukkanin ɗiyoyin da aka kawo an juya su ne kamar yadda aka rubuta su a littattafan da aka yi nazari a cikinsu.
Takardar ta gano Alhaji Sa’idu Faru yakan yabi duk wani wanda ya yi masa alkhairi ko aka yi masa alkhairi saboda shi.
Haka kuma an gano irin zuga da yake yi wa wanda ya zaɓi ya yi masa waƙa, yakan nuna hazaƙarsa da bajintarsa da fasaharsa wajen kwarzanta da zuga duk abin da ya so ya yi wa waƙa.
Takardar ta yi ƙoƙarin sharhanta wasu daga cikin ɗiyan da ya bayyana zuga da yabo a cikinsu.

Related Results

Salon Jerin Sarƙe a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
Salon Jerin Sarƙe a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
Masana sun tabbatar da cewa, Salo ya ƙunshi duk wasu dabaru da hikimomin jawo hankali domin a isar da saƙo cikin harshe mai burgewa da saka karsashi da kuma jawo hankali ga mai sau...
Zambo A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u
Zambo A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u
A kowane lokaci adabin al’uma kan fayyace yadda rayuwa da tsarin zamantakewar al’umar ke wakana ne, ta yadda ake sa rai idan an dubi adabin wannnan al’umar a iya hango hoton rayuwa...
Wasu Ƙananan Tubalan Turken Yabon Mata a Zubin Wasu Waƙoƙin Shata
Wasu Ƙananan Tubalan Turken Yabon Mata a Zubin Wasu Waƙoƙin Shata
Yabo na cikin manyan turakun da makaɗan baka suka fi yawaita yin waƙoƙi na baka a kan sa. Kusan shi ne ma fitaccen turken waƙoƙin baka na Hausa domin mafi yawan waƙoƙin manufofinsu...
Kirari A Wasu Waƙoƙin Makaɗan Maza
Kirari A Wasu Waƙoƙin Makaɗan Maza
Wannan takarda mai suna “kirari a wasu waƙoƙin makaɗan maza” ta ƙunshi ma’anar kirari daga masana daban-daban, da rabe-raben kirari tare da fito da yanayinsa da sigoginsa da kuma y...
Salon Tsattsafi a Cikin Wasu Waƙoƙin Maryam Sale Fantimoti
Salon Tsattsafi a Cikin Wasu Waƙoƙin Maryam Sale Fantimoti
Makaɗan baka na Hausa kan yi amfani da hikima, da basirar da Allah ya yi musu wajen tsara maganganun, da za su ja hankalin mai sauraro ta hanyar amfani da adon harshe. Maryam Sale ...
Humoral dysregulation among injection drug users: implications for HIV vaccine strategies (VAC11P.1103)
Humoral dysregulation among injection drug users: implications for HIV vaccine strategies (VAC11P.1103)
Abstract The primary objective of a preventative HIV vaccine is the induction of a persistent humoral response that mediates sterilizing immunity. Although modest, y...
Kwatanta Tubalan Gina Turken Waƙar ‘Hauwa Maituwo ta Mamman Shata Katsina da ta Tafada Mai Tuwo ta Mamman Gawo Filinge
Kwatanta Tubalan Gina Turken Waƙar ‘Hauwa Maituwo ta Mamman Shata Katsina da ta Tafada Mai Tuwo ta Mamman Gawo Filinge
Wannan bincike an aiwatar da shi a kan waƙoƙin fitattun mawaƙan Hausa guda biyu (Mamman Shata Katsina na Nijeriya da Mamman Gawo Filinge na Jamhuriyar Nijar). Waƙar Mamman Shata da...
“We Own Kano and Kano Owns Us”: Politics, Place, and Identity in Independence-Era Kano
“We Own Kano and Kano Owns Us”: Politics, Place, and Identity in Independence-Era Kano
Abstract The short period leading up to and following Nigerian independence was one of dramatic political maneuvering and change in Nigeria’s Northern Region. For mu...

Back to Top