Search engine for discovering works of Art, research articles, and books related to Art and Culture
ShareThis
Javascript must be enabled to continue!

Hannu Ba Ka Da Tsoro: Gurbin Hannu Cikin Tunanin Masu Abu “Hausawa”

View through CrossRef
Tunanin wannan bincike shi ne, fayyace yadda sunan hannu ya yi naso da malkashi cikin tunanin Bahaushe da ke bayyana cikin adabinsa, da al’adunsa, da harshensa. Binciken da aka yi na take da kirarin da Bahaushe ke yi wa hannu, na cewa ba ya da tsoro. An yi amfani da kayayyakin adabi da al’ada da harshe domin tabbatar da dugadugan bincike. Karance-karancen ayyukan magabata kawai ba zai warkar ba, dole sai an haɗa da yawon rangadi da tattauna na rukunin mutane daban-daban. Da aka fahinci babu wani aiki bugagge ko wani ba shi ba da aka yi a kan Bahaushen tunani kan hannu sai aka kwakkwahe takardun rubutu. An ɗora wannan ‘yar takarda bisa fasula (13) haɗe da gabatarwa da naɗewa. Takarda ta yi wa hannu karatun ƙwaƙƙwafi bayan fayyace suna (2) na hannaye, ta sake ƙwalailaice abubuwa (15) da ke liƙe ga hannun ɗan Adam da sunayen da Bahaushe ya laƙaba musu. A jimlace an leƙo amfanonin hannu (23) tare da fayyace nau’o’in rabe-raben hannu (9) a Hausance, An kafa hujja da sassan adabi (23) da suka ambaci hannu a mahanga mabambanta, tare da amfani da ɗiyan waƙa (7) na mawaƙan baka daban-daban domin kwakkwahe bayani. Labaran raha (2) aka yi garkuwa da su na tabbatar da samuwar shawagin hannu cikin tunanin Bahaushe. A jimlace an sarrafa haujjoji (81) da suka tabbatar da da’awar wannan bincike. A kan haka, binciken ya hango sakamako (5) da aka rairaye cewa, babu wata gaɓa daga cikin gaɓɓan ɗan Adam da ta kai hannu tasiri cikin tunaninsa. Don haka ya zama jagora daga cikin gaɓɓan ɗan Adam. Tabbas! Yadda Bahaushe ke kallon bahagon hannu haka nan yake a addinance da kimiyance. A kan haka ne wannan takarda ke da fahintar ya kyautu a saka nazarin sassan gaɓoɓin jikin ɗan Adam cikin manhajar koyarwar harsunanmu. Akwai buƙatar mayar da himma ga wannan fanni na nazari.
Title: Hannu Ba Ka Da Tsoro: Gurbin Hannu Cikin Tunanin Masu Abu “Hausawa”
Description:
Tunanin wannan bincike shi ne, fayyace yadda sunan hannu ya yi naso da malkashi cikin tunanin Bahaushe da ke bayyana cikin adabinsa, da al’adunsa, da harshensa.
Binciken da aka yi na take da kirarin da Bahaushe ke yi wa hannu, na cewa ba ya da tsoro.
An yi amfani da kayayyakin adabi da al’ada da harshe domin tabbatar da dugadugan bincike.
Karance-karancen ayyukan magabata kawai ba zai warkar ba, dole sai an haɗa da yawon rangadi da tattauna na rukunin mutane daban-daban.
Da aka fahinci babu wani aiki bugagge ko wani ba shi ba da aka yi a kan Bahaushen tunani kan hannu sai aka kwakkwahe takardun rubutu.
An ɗora wannan ‘yar takarda bisa fasula (13) haɗe da gabatarwa da naɗewa.
Takarda ta yi wa hannu karatun ƙwaƙƙwafi bayan fayyace suna (2) na hannaye, ta sake ƙwalailaice abubuwa (15) da ke liƙe ga hannun ɗan Adam da sunayen da Bahaushe ya laƙaba musu.
A jimlace an leƙo amfanonin hannu (23) tare da fayyace nau’o’in rabe-raben hannu (9) a Hausance, An kafa hujja da sassan adabi (23) da suka ambaci hannu a mahanga mabambanta, tare da amfani da ɗiyan waƙa (7) na mawaƙan baka daban-daban domin kwakkwahe bayani.
Labaran raha (2) aka yi garkuwa da su na tabbatar da samuwar shawagin hannu cikin tunanin Bahaushe.
A jimlace an sarrafa haujjoji (81) da suka tabbatar da da’awar wannan bincike.
A kan haka, binciken ya hango sakamako (5) da aka rairaye cewa, babu wata gaɓa daga cikin gaɓɓan ɗan Adam da ta kai hannu tasiri cikin tunaninsa.
Don haka ya zama jagora daga cikin gaɓɓan ɗan Adam.
Tabbas! Yadda Bahaushe ke kallon bahagon hannu haka nan yake a addinance da kimiyance.
A kan haka ne wannan takarda ke da fahintar ya kyautu a saka nazarin sassan gaɓoɓin jikin ɗan Adam cikin manhajar koyarwar harsunanmu.
Akwai buƙatar mayar da himma ga wannan fanni na nazari.

Related Results

Zambo A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u
Zambo A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u
A kowane lokaci adabin al’uma kan fayyace yadda rayuwa da tsarin zamantakewar al’umar ke wakana ne, ta yadda ake sa rai idan an dubi adabin wannnan al’umar a iya hango hoton rayuwa...
Tarbiya a Falsafar Al’ada
Tarbiya a Falsafar Al’ada
Al’ummar Hausawa sun daɗe suna gudanar da harkokin rayuwarsu kamar yadda al’adarsu ta tanada. Kowace al’umma haka ake sa ran takasance tana alfahari da al’adunta. Tarbiya tana daga...
Penentuan Kandungan Logam Magnetik Komponen Penyusun Abu Layang Batubara
Penentuan Kandungan Logam Magnetik Komponen Penyusun Abu Layang Batubara
Telah dilakukan penelitian penentuan kandungan logam magnetik penyusun abu layang batubara. Abu layang merupakan material berupa serbuk halus yang dihasilkan dari pembakaran batuba...
Gudummawar Rubutattun Waƙoƙin Hausa ta Fuskar Faɗakarwa Wajen Kyautata Zamantakewar Hausawa
Gudummawar Rubutattun Waƙoƙin Hausa ta Fuskar Faɗakarwa Wajen Kyautata Zamantakewar Hausawa
Masu hikima na yin amfani da adabin baka wajen sarrafa harshen Hausa don sauran mutane masu magana da kuma amfani da harshen Hausa su saurara su kuma more wajen samun zantuttuka ma...
Izga Da Matsayinta a Bahaushiyar Al’ada
Izga Da Matsayinta a Bahaushiyar Al’ada
Munafar wannan takarda ita ce fito da amfanin izga a tunanin Hausawa a wajen amfani na yau da kullum da kuma wajen magance wasu cututtuka, musamman a mahangar ‘yanbori. Haka kuma, ...
Salon Jerin Sarƙe a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
Salon Jerin Sarƙe a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
Masana sun tabbatar da cewa, Salo ya ƙunshi duk wasu dabaru da hikimomin jawo hankali domin a isar da saƙo cikin harshe mai burgewa da saka karsashi da kuma jawo hankali ga mai sau...
Tanadin Tatsuniyoyin Hausa wajen Tabbatar da Zaman Lafiya
Tanadin Tatsuniyoyin Hausa wajen Tabbatar da Zaman Lafiya
Hausawa na cewa “zaman lafiya mai daɗi”. Tatsuniya tana daga cikin fannonin adabi da suka game duniya baki ɗaya, saboda a kowane harshe da ke cikin faɗin duniya komai ƙanƙantarsa d...
Salon Tsattsafi a Cikin Wasu Waƙoƙin Maryam Sale Fantimoti
Salon Tsattsafi a Cikin Wasu Waƙoƙin Maryam Sale Fantimoti
Makaɗan baka na Hausa kan yi amfani da hikima, da basirar da Allah ya yi musu wajen tsara maganganun, da za su ja hankalin mai sauraro ta hanyar amfani da adon harshe. Maryam Sale ...

Back to Top