Javascript must be enabled to continue!
Tarken Yabo da Zuga a cikin wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru
View through CrossRef
Yabo a fagen waƙa wasu kalamai ne da ake yi domin faranta ran wanda ake yi wa waƙa. Zuga kuma ita ce ingiza ko kwarzanta wanda ake yabawa a cikin waƙa. Makaɗa Sa'idu Faru fitaccen mawaƙin baka ne a ƙasar Hausa wanda ya ƙware sosai wajen kiɗan fada. Manufar wannan maƙala ita ce; Fito da yabo da zuga a wasu waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru da kuna kalmomin yabo da zuga da makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da su a kan mizanin fahimtar masu sauraronsa. Sai kuma, nazartar kalmomin yabo da zuga a cikin wasu waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru. An yi amfani da hanyar hira da ma’abota ilimi musamman abin da ya ƙunshi waƙar baka. Haka kuma an yi amfani da hanyar sauraron wasu daga cikin waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru domin samun hujjojin gina wannan maƙala. Ba wannan kaɗai ba, maƙalar ta yi amfani da hanyar karance-karancen bugaggun littattafai da kundaye da mujallu da maƙalun da aka gabatar domin ƙara wa juna sani wajen samun hujjojin da suka gina wannan maƙala. Hanyar dora aikin da aka yi amfani da ita kuwa, ita ce mazhabar waƙar baka Bahaushiya. Sakamakon wannan bincike ya gano cewa, mafi yawan waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru suna ƙunshe da yabo da zuga ga sarakuna. Sannan kuma, nauyin wannan yabo ko zuga suna yin tasiri matuƙa ga zukatan masu sauraro. A ɓangaren mizanin al’ada kuwa, ana danganta wannan yabo da zuga asali da jarumtakar sarakuna. Har ila yau, yin wannan yabo ko zuga yana nuna nauyin yadda makaɗin yake ɗaukar masu gidansa.
SASPR Edu International Pvt. Ltd
Title: Tarken Yabo da Zuga a cikin wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru
Description:
Yabo a fagen waƙa wasu kalamai ne da ake yi domin faranta ran wanda ake yi wa waƙa.
Zuga kuma ita ce ingiza ko kwarzanta wanda ake yabawa a cikin waƙa.
Makaɗa Sa'idu Faru fitaccen mawaƙin baka ne a ƙasar Hausa wanda ya ƙware sosai wajen kiɗan fada.
Manufar wannan maƙala ita ce; Fito da yabo da zuga a wasu waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru da kuna kalmomin yabo da zuga da makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da su a kan mizanin fahimtar masu sauraronsa.
Sai kuma, nazartar kalmomin yabo da zuga a cikin wasu waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru.
An yi amfani da hanyar hira da ma’abota ilimi musamman abin da ya ƙunshi waƙar baka.
Haka kuma an yi amfani da hanyar sauraron wasu daga cikin waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru domin samun hujjojin gina wannan maƙala.
Ba wannan kaɗai ba, maƙalar ta yi amfani da hanyar karance-karancen bugaggun littattafai da kundaye da mujallu da maƙalun da aka gabatar domin ƙara wa juna sani wajen samun hujjojin da suka gina wannan maƙala.
Hanyar dora aikin da aka yi amfani da ita kuwa, ita ce mazhabar waƙar baka Bahaushiya.
Sakamakon wannan bincike ya gano cewa, mafi yawan waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru suna ƙunshe da yabo da zuga ga sarakuna.
Sannan kuma, nauyin wannan yabo ko zuga suna yin tasiri matuƙa ga zukatan masu sauraro.
A ɓangaren mizanin al’ada kuwa, ana danganta wannan yabo da zuga asali da jarumtakar sarakuna.
Har ila yau, yin wannan yabo ko zuga yana nuna nauyin yadda makaɗin yake ɗaukar masu gidansa.
Related Results
Turken Zuga da Yabo a Zubin Wasu Ɗiyan Waƙoƙin Alhaji Sa’idu Faru: Nazari DagaWaƙar Turakin Kano Alhaji Ahmadu
Turken Zuga da Yabo a Zubin Wasu Ɗiyan Waƙoƙin Alhaji Sa’idu Faru: Nazari DagaWaƙar Turakin Kano Alhaji Ahmadu
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin turken zuga da yabo a waƙar Turakin Kano. Don haka zuga ko yabo ɗaya ne daga cikin turakun waƙoƙin makaɗan baka na Hausa, musam...
Salon Jerin Sarƙe a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
Salon Jerin Sarƙe a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
Masana sun tabbatar da cewa, Salo ya ƙunshi duk wasu dabaru da hikimomin jawo hankali domin a isar da saƙo cikin harshe mai burgewa da saka karsashi da kuma jawo hankali ga mai sau...
Zambo A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u
Zambo A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u
A kowane lokaci adabin al’uma kan fayyace yadda rayuwa da tsarin zamantakewar al’umar ke wakana ne, ta yadda ake sa rai idan an dubi adabin wannnan al’umar a iya hango hoton rayuwa...
Salon Sakaɗe a Waƙoƙin Baka na Hausa: Duba Cikin Wasu Shahararrun Waƙoƙin Mashahuran Mawaƙan Baka
Salon Sakaɗe a Waƙoƙin Baka na Hausa: Duba Cikin Wasu Shahararrun Waƙoƙin Mashahuran Mawaƙan Baka
Burin wannan bincike lalubo wani salo daga cikin salailai da mawaƙan baka ke amfani da su
wajen isar da saƙonsu ga masu sauraron su. An yi wa binciken take “Salon Sakaɗe: an ƙago s...
Nazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu Waƙoƙin Siyasa na Hausa
Nazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu Waƙoƙin Siyasa na Hausa
Wannan takarda mai takenNazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu waƙoƙin siyasa na Hausa,n rubuta ta ne da niyyar fito da ire-iren hikimomi da basirar da mawallafan siyasa suke amfani da ...
Salon Tsattsafi a Cikin Wasu Waƙoƙin Maryam Sale Fantimoti
Salon Tsattsafi a Cikin Wasu Waƙoƙin Maryam Sale Fantimoti
Makaɗan baka na Hausa kan yi amfani da hikima, da basirar da Allah ya yi musu wajen tsara maganganun, da za su ja hankalin mai sauraro ta hanyar amfani da adon harshe. Maryam Sale ...
Kirari A Wasu Waƙoƙin Makaɗan Maza
Kirari A Wasu Waƙoƙin Makaɗan Maza
Wannan takarda mai suna “kirari a wasu waƙoƙin makaɗan maza” ta ƙunshi ma’anar kirari daga masana daban-daban, da rabe-raben kirari tare da fito da yanayinsa da sigoginsa da kuma y...
Wasu Ƙananan Tubalan Turken Yabon Mata a Zubin Wasu Waƙoƙin Shata
Wasu Ƙananan Tubalan Turken Yabon Mata a Zubin Wasu Waƙoƙin Shata
Yabo na cikin manyan turakun da makaɗan baka suka fi yawaita yin waƙoƙi na baka a kan sa. Kusan shi ne ma fitaccen turken waƙoƙin baka na Hausa domin mafi yawan waƙoƙin manufofinsu...

