Javascript must be enabled to continue!
Nazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu Waƙoƙin Siyasa na Hausa
View through CrossRef
Wannan takarda mai takenNazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu waƙoƙin siyasa na Hausa,n rubuta ta ne da niyyar fito da ire-iren hikimomi da basirar da mawallafan siyasa suke amfani da su ta hanyar ɗaukar abin da ba mutum ba su mayar da shi mutum domin su isar da saƙonsu ga jama’a ta hanyar hikima a cikin waƙoƙinsu na siyasa. A nazarin an yi amfani da waƙoƙi a ƙalla guda goma sha biyu na mawallafa daban-daban waɗanda suka yi amfani da wannan dabarar a cikin waƙoƙin. An ɗora wannan takarda bisa hanyar nazari wadda Ɗangambo (2007) ya assasa a littafinsa na Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa. An yi amfani da dabaru da hanyoyin wajen gudanar da wannan nazari waɗanda suka haɗa da samo waƙoƙin daga hannun wasu mawallafan, an kuma samu waƙoƙin daga wasu kundayen bincike na ilimi a matakai daban-daban a kuma rubuce. A nazarin an gano mawallafan sun yi amfani da wannan dabarar ta hanyar yin amfani da wasu siffofi da darajoji da halaye da sauransu da mutum kaɗai aka sani da su a laƙaba wa wanda ba mutum ba ya zama mutum, domin su isar da saƙo ga masu saurare ko karatu a cikin waƙoƙinsu. Haka kuma an yi nasarar fito da ire-iren misalai na dabarar mutuntarwa ta hali da mutuntarwa ta siffa da mutuntarwa ta daraja tare da yi musu sharhi. Har ila yau kuma, ana kyautata zaton wannan nazarin zai zama jagora a kan abin da ya shafi dabarun jawo hankali musamman na mutuntarwa a waƙoƙin siyasa a fannin adabin Hausa. Haka kuma nazarin ya zamto jagora ga manazarta da ɗalibai a ɓangaren rubutattun waƙoƙi musamman na siyasa a fannin adabin Hausa.
SASPR Edu International Pvt. Ltd
Title: Nazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu Waƙoƙin Siyasa na Hausa
Description:
Wannan takarda mai takenNazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu waƙoƙin siyasa na Hausa,n rubuta ta ne da niyyar fito da ire-iren hikimomi da basirar da mawallafan siyasa suke amfani da su ta hanyar ɗaukar abin da ba mutum ba su mayar da shi mutum domin su isar da saƙonsu ga jama’a ta hanyar hikima a cikin waƙoƙinsu na siyasa.
A nazarin an yi amfani da waƙoƙi a ƙalla guda goma sha biyu na mawallafa daban-daban waɗanda suka yi amfani da wannan dabarar a cikin waƙoƙin.
An ɗora wannan takarda bisa hanyar nazari wadda Ɗangambo (2007) ya assasa a littafinsa na Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa.
An yi amfani da dabaru da hanyoyin wajen gudanar da wannan nazari waɗanda suka haɗa da samo waƙoƙin daga hannun wasu mawallafan, an kuma samu waƙoƙin daga wasu kundayen bincike na ilimi a matakai daban-daban a kuma rubuce.
A nazarin an gano mawallafan sun yi amfani da wannan dabarar ta hanyar yin amfani da wasu siffofi da darajoji da halaye da sauransu da mutum kaɗai aka sani da su a laƙaba wa wanda ba mutum ba ya zama mutum, domin su isar da saƙo ga masu saurare ko karatu a cikin waƙoƙinsu.
Haka kuma an yi nasarar fito da ire-iren misalai na dabarar mutuntarwa ta hali da mutuntarwa ta siffa da mutuntarwa ta daraja tare da yi musu sharhi.
Har ila yau kuma, ana kyautata zaton wannan nazarin zai zama jagora a kan abin da ya shafi dabarun jawo hankali musamman na mutuntarwa a waƙoƙin siyasa a fannin adabin Hausa.
Haka kuma nazarin ya zamto jagora ga manazarta da ɗalibai a ɓangaren rubutattun waƙoƙi musamman na siyasa a fannin adabin Hausa.
Related Results
Harshe Makamin Siyasa: Nazarin Yabo da Suka cikin Waƙoƙin Siyasa
Harshe Makamin Siyasa: Nazarin Yabo da Suka cikin Waƙoƙin Siyasa
Harshe yana ɗaya daga cikin tarin baiwar da Allah (S.W.T) ya hore wa ɗan Adam, wanda ake amfani da shi wajen sadarwa musamman ta hanyar yin magana ko waƙa ko hira da dai sauransu. ...
Hamayya ko Adawa a Cikin Waƙoƙin Siyasa a Ƙasar Hausa
Hamayya ko Adawa a Cikin Waƙoƙin Siyasa a Ƙasar Hausa
Waƙa a siyasa kamar gishiri ne a cikin miya, rukuni ne kuma ginshiƙi ne babba a cikin harkokin siyasa, kusan a iya cewa, siyasa ba ta zama da ƙafafunta ba tare da waƙa ba (Usman 20...
Salon Jerin Sarƙe a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
Salon Jerin Sarƙe a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
Masana sun tabbatar da cewa, Salo ya ƙunshi duk wasu dabaru da hikimomin jawo hankali domin a isar da saƙo cikin harshe mai burgewa da saka karsashi da kuma jawo hankali ga mai sau...
Nazarin Rikiɗar Wasu Sautukan Harshen Ngizim Zuwa Hausa
Nazarin Rikiɗar Wasu Sautukan Harshen Ngizim Zuwa Hausa
A duk lokacin da aka samu wata cuɗanya ta mu’amala tsakanin harsuna mabambanta guda biyu, akan samu harshe mafi tasiri a tsakaninsu. Irin wannan dangantaka ta tsakanin harsuna, ita...
Salon Sakaɗe a Waƙoƙin Baka na Hausa: Duba Cikin Wasu Shahararrun Waƙoƙin Mashahuran Mawaƙan Baka
Salon Sakaɗe a Waƙoƙin Baka na Hausa: Duba Cikin Wasu Shahararrun Waƙoƙin Mashahuran Mawaƙan Baka
Burin wannan bincike lalubo wani salo daga cikin salailai da mawaƙan baka ke amfani da su
wajen isar da saƙonsu ga masu sauraron su. An yi wa binciken take “Salon Sakaɗe: an ƙago s...
Nazarin Tsarin Sauti a Wasu Zaurance Na Hausa
Nazarin Tsarin Sauti a Wasu Zaurance Na Hausa
Zaurance yana ɗaya daga cikin azancin da harshen Hausa ya yi fice da su wanda matasa musamman mata suke amfani da shi wajen sakaya zance ta hanyar sauya masa wasu fitattun kamannin...
Sarrafa Harshen Mawallafiya a Matsayin Dabarar Bayar da Labari a Wasu Ƙagaggun Rubutattun Labaran Hausa na Balaraba Ramat Yakubu
Sarrafa Harshen Mawallafiya a Matsayin Dabarar Bayar da Labari a Wasu Ƙagaggun Rubutattun Labaran Hausa na Balaraba Ramat Yakubu
Wannan aiki yana ƙunshe da bayanai dangane da yadda mawallafiya ta yi amfani da dabarar sarrafa harshe domin ta yaɗa wasu al’adun Hausawa da kuma na wasu al’ummomin da ba Hausawa b...

