Javascript must be enabled to continue!
Harshe Makamin Siyasa: Nazarin Yabo da Suka cikin Waƙoƙin Siyasa
View through CrossRef
Harshe yana ɗaya daga cikin tarin baiwar da Allah (S.W.T) ya hore wa ɗan Adam, wanda ake amfani da shi wajen sadarwa musamman ta hanyar yin magana ko waƙa ko hira da dai sauransu. Harshe yana daga cikin muhimman abubuwan da ake amfani da su a fagen siyasa, wanda hakan yakan taimaka wurin samun nasara ko akasin haka. Mawaƙan siyasa da dama sukan yi amfani da irin baiwar da Allah ya ba su na iya sarrafa kalmomi a waƙe wajen yabon jam’iyyarsu ko ‘ya’yanta, domin ɗaga su da tallata su ga sauran jama’a. Haka kuma da irin wannan baiwar ce suke amfani wajen sukar ‘yan adawa da jam’iyyar adawar domin dusashe haskensu. Wannan takarda ta yi nazarin yadda ake amfani da waƙoƙin siyasa wajen yabon jam’iyya da shugabanninta da kuma ƙoƙarin daƙushe hasken jam’iyyar adawa da magoya bayanta. A ƙarshe binciken ya gano cewa harshe wani ginshiƙi ne wajen tafiyar da al’amuran siyasa domin da shi ne ake tallata jam’iyya ko ɗan takara har su karɓu ga jama’a, kuma da shi ne ake kushe su ta hanyar suka wanda hakan kan rage musu farin jini ko ya janyo su rasa magoya baya. A cikin nazarin an riƙa kawo misalai daga baitocin waƙoƙin siyasa domin kafa hujja.
Title: Harshe Makamin Siyasa: Nazarin Yabo da Suka cikin Waƙoƙin Siyasa
Description:
Harshe yana ɗaya daga cikin tarin baiwar da Allah (S.
W.
T) ya hore wa ɗan Adam, wanda ake amfani da shi wajen sadarwa musamman ta hanyar yin magana ko waƙa ko hira da dai sauransu.
Harshe yana daga cikin muhimman abubuwan da ake amfani da su a fagen siyasa, wanda hakan yakan taimaka wurin samun nasara ko akasin haka.
Mawaƙan siyasa da dama sukan yi amfani da irin baiwar da Allah ya ba su na iya sarrafa kalmomi a waƙe wajen yabon jam’iyyarsu ko ‘ya’yanta, domin ɗaga su da tallata su ga sauran jama’a.
Haka kuma da irin wannan baiwar ce suke amfani wajen sukar ‘yan adawa da jam’iyyar adawar domin dusashe haskensu.
Wannan takarda ta yi nazarin yadda ake amfani da waƙoƙin siyasa wajen yabon jam’iyya da shugabanninta da kuma ƙoƙarin daƙushe hasken jam’iyyar adawa da magoya bayanta.
A ƙarshe binciken ya gano cewa harshe wani ginshiƙi ne wajen tafiyar da al’amuran siyasa domin da shi ne ake tallata jam’iyya ko ɗan takara har su karɓu ga jama’a, kuma da shi ne ake kushe su ta hanyar suka wanda hakan kan rage musu farin jini ko ya janyo su rasa magoya baya.
A cikin nazarin an riƙa kawo misalai daga baitocin waƙoƙin siyasa domin kafa hujja.
Related Results
Nazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu Waƙoƙin Siyasa na Hausa
Nazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu Waƙoƙin Siyasa na Hausa
Wannan takarda mai takenNazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu waƙoƙin siyasa na Hausa,n rubuta ta ne da niyyar fito da ire-iren hikimomi da basirar da mawallafan siyasa suke amfani da ...
Tarken Yabo da Zuga a cikin wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru
Tarken Yabo da Zuga a cikin wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru
Yabo a fagen waƙa wasu kalamai ne da ake yi domin faranta ran wanda ake yi wa waƙa. Zuga kuma ita ce ingiza ko kwarzanta wanda ake yabawa a cikin waƙa. Makaɗa Sa'idu Faru fitaccen ...
Salon Sakaɗe a Waƙoƙin Baka na Hausa: Duba Cikin Wasu Shahararrun Waƙoƙin Mashahuran Mawaƙan Baka
Salon Sakaɗe a Waƙoƙin Baka na Hausa: Duba Cikin Wasu Shahararrun Waƙoƙin Mashahuran Mawaƙan Baka
Burin wannan bincike lalubo wani salo daga cikin salailai da mawaƙan baka ke amfani da su
wajen isar da saƙonsu ga masu sauraron su. An yi wa binciken take “Salon Sakaɗe: an ƙago s...
Zambo A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u
Zambo A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u
A kowane lokaci adabin al’uma kan fayyace yadda rayuwa da tsarin zamantakewar al’umar ke wakana ne, ta yadda ake sa rai idan an dubi adabin wannnan al’umar a iya hango hoton rayuwa...
Salo Ruhin Waƙa: Nazarin Salo a Waƙar ‘Salo’ Ta Alhaji Sani Sabulu Kanoma
Salo Ruhin Waƙa: Nazarin Salo a Waƙar ‘Salo’ Ta Alhaji Sani Sabulu Kanoma
Waƙa kamar yadda masana suka yi ta ƙoƙarin bayyanawa zance ne da ya saɓa da zance na yau da kullum domin ita shiryayyiyar magana ce mai ƙunshe da saƙo wadda ake aiwatarwa cikin hik...
Hamayya ko Adawa a Cikin Waƙoƙin Siyasa a Ƙasar Hausa
Hamayya ko Adawa a Cikin Waƙoƙin Siyasa a Ƙasar Hausa
Waƙa a siyasa kamar gishiri ne a cikin miya, rukuni ne kuma ginshiƙi ne babba a cikin harkokin siyasa, kusan a iya cewa, siyasa ba ta zama da ƙafafunta ba tare da waƙa ba (Usman 20...
Salon Tsattsafi a Cikin Wasu Waƙoƙin Maryam Sale Fantimoti
Salon Tsattsafi a Cikin Wasu Waƙoƙin Maryam Sale Fantimoti
Makaɗan baka na Hausa kan yi amfani da hikima, da basirar da Allah ya yi musu wajen tsara maganganun, da za su ja hankalin mai sauraro ta hanyar amfani da adon harshe. Maryam Sale ...
Hannu Ba Ka Da Tsoro: Gurbin Hannu Cikin Tunanin Masu Abu “Hausawa”
Hannu Ba Ka Da Tsoro: Gurbin Hannu Cikin Tunanin Masu Abu “Hausawa”
Tunanin wannan bincike shi ne, fayyace yadda sunan hannu ya yi naso da malkashi cikin tunanin Bahaushe da ke bayyana cikin adabinsa, da al’adunsa, da harshensa. Binciken da aka yi ...

