Javascript must be enabled to continue!
Hamayya ko Adawa a Cikin Waƙoƙin Siyasa a Ƙasar Hausa
View through CrossRef
Waƙa a siyasa kamar gishiri ne a cikin miya, rukuni ne kuma ginshiƙi ne babba a cikin harkokin siyasa, kusan a iya cewa, siyasa ba ta zama da ƙafafunta ba tare da waƙa ba (Usman 2013:3). Jam’iyyun siyasa sukan yi amfani da waƙoƙi domin yin kamfe, wanda a cikinsu ne suke bayyana manufofinsu da yin suka, da kawo hanyoyin gyara ko yin zambo har ma da zagi ga abokan hamayya ko tsakanin jam’iyyu biyu (Adamu 2003:54). Ta ɗaya hannun kuma akan sami waƙoƙi masu yin ɓatanci ga wata jam’iyya ko magoya bayan jam’iyya wani lokaci har da cin mutunci da zagi da yin fito-na-fito da zambo ta yadda manufar ta kauce hanyar hamayya ta zama adawa. A siyasance kalmar “Hamayya” ya kamata a yi amfani da ita wadda ba ta hana jituwa tsakanin ‘yan siyasa. Ba Kalmar “Adawa” ba mai manufar ƙiyayya ta har abada. Manufar wannan takarda ce, ƙoƙarin kawo manufofi na adawa maimaikon hamayya kamar yadda aka tsinkayi hakan a cikin wasu waƙoƙin siyasa a ƙasar Hausa domin faɗakarwa.
Title: Hamayya ko Adawa a Cikin Waƙoƙin Siyasa a Ƙasar Hausa
Description:
Waƙa a siyasa kamar gishiri ne a cikin miya, rukuni ne kuma ginshiƙi ne babba a cikin harkokin siyasa, kusan a iya cewa, siyasa ba ta zama da ƙafafunta ba tare da waƙa ba (Usman 2013:3).
Jam’iyyun siyasa sukan yi amfani da waƙoƙi domin yin kamfe, wanda a cikinsu ne suke bayyana manufofinsu da yin suka, da kawo hanyoyin gyara ko yin zambo har ma da zagi ga abokan hamayya ko tsakanin jam’iyyu biyu (Adamu 2003:54).
Ta ɗaya hannun kuma akan sami waƙoƙi masu yin ɓatanci ga wata jam’iyya ko magoya bayan jam’iyya wani lokaci har da cin mutunci da zagi da yin fito-na-fito da zambo ta yadda manufar ta kauce hanyar hamayya ta zama adawa.
A siyasance kalmar “Hamayya” ya kamata a yi amfani da ita wadda ba ta hana jituwa tsakanin ‘yan siyasa.
Ba Kalmar “Adawa” ba mai manufar ƙiyayya ta har abada.
Manufar wannan takarda ce, ƙoƙarin kawo manufofi na adawa maimaikon hamayya kamar yadda aka tsinkayi hakan a cikin wasu waƙoƙin siyasa a ƙasar Hausa domin faɗakarwa.
Related Results
Nazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu Waƙoƙin Siyasa na Hausa
Nazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu Waƙoƙin Siyasa na Hausa
Wannan takarda mai takenNazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu waƙoƙin siyasa na Hausa,n rubuta ta ne da niyyar fito da ire-iren hikimomi da basirar da mawallafan siyasa suke amfani da ...
Harshe Makamin Siyasa: Nazarin Yabo da Suka cikin Waƙoƙin Siyasa
Harshe Makamin Siyasa: Nazarin Yabo da Suka cikin Waƙoƙin Siyasa
Harshe yana ɗaya daga cikin tarin baiwar da Allah (S.W.T) ya hore wa ɗan Adam, wanda ake amfani da shi wajen sadarwa musamman ta hanyar yin magana ko waƙa ko hira da dai sauransu. ...
Tasirin Mawaƙan Baka Wajen Haɓaka Al-Adun Hausawa
Tasirin Mawaƙan Baka Wajen Haɓaka Al-Adun Hausawa
Ƙasar Hausa kamar yadda tarihinta ya zo a litattafai da dama, suna alaƙanta ta da mazaunin Hausawa na farko kafin su watsu zuwa sassa daban-daban na duniya. Mu’azu (1993:1) ya bayy...
Salon Sakaɗe a Waƙoƙin Baka na Hausa: Duba Cikin Wasu Shahararrun Waƙoƙin Mashahuran Mawaƙan Baka
Salon Sakaɗe a Waƙoƙin Baka na Hausa: Duba Cikin Wasu Shahararrun Waƙoƙin Mashahuran Mawaƙan Baka
Burin wannan bincike lalubo wani salo daga cikin salailai da mawaƙan baka ke amfani da su
wajen isar da saƙonsu ga masu sauraron su. An yi wa binciken take “Salon Sakaɗe: an ƙago s...
Zambo A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u
Zambo A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u
A kowane lokaci adabin al’uma kan fayyace yadda rayuwa da tsarin zamantakewar al’umar ke wakana ne, ta yadda ake sa rai idan an dubi adabin wannnan al’umar a iya hango hoton rayuwa...
Salon Tsattsafi a Cikin Wasu Waƙoƙin Maryam Sale Fantimoti
Salon Tsattsafi a Cikin Wasu Waƙoƙin Maryam Sale Fantimoti
Makaɗan baka na Hausa kan yi amfani da hikima, da basirar da Allah ya yi musu wajen tsara maganganun, da za su ja hankalin mai sauraro ta hanyar amfani da adon harshe. Maryam Sale ...
Tarken Yabo da Zuga a cikin wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru
Tarken Yabo da Zuga a cikin wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru
Yabo a fagen waƙa wasu kalamai ne da ake yi domin faranta ran wanda ake yi wa waƙa. Zuga kuma ita ce ingiza ko kwarzanta wanda ake yabawa a cikin waƙa. Makaɗa Sa'idu Faru fitaccen ...

