Javascript must be enabled to continue!
Salon Tsattsafi a Cikin Wasu Waƙoƙin Maryam Sale Fantimoti
View through CrossRef
Makaɗan baka na Hausa kan yi amfani da hikima, da basirar da Allah ya yi musu wajen tsara maganganun, da za su ja hankalin mai sauraro ta hanyar amfani da adon harshe. Maryam Sale Fantimoti na ɗaya daga makaɗan da Allah ya horewa wannan baiwa, da hikima da zalaƙar zance. A wannan nazari an kalli yadda Maryam Sale Fantimoti ta yi amfani da dabaran adon harshe ta salon tsattsafi a wasu daga cikin waƙoƙinta. An ɗora binciken bisa ra’in ƙaye (Aethtetic theory). Dabaru da hanyoyin da ake bi wajen gudanar da wannan nazari sun haɗa da, tattaunawa da Maryam Sale Fantimoti da wasu masana. Binciken ya gano Maryam Sale Fantimoti tana amfani da tsattsafin haliyya wanda kan haifar da raha da soyayya da farin ciki da baƙin ciki, da sauran halaye da mutane kan tsinci kan su a ciki, dukkanninsu a cikin waƙoƙin nata. Manufar wannan takarda ita ce, jawo hankalin ɗalibai ‘yan’uwana da manazarta da ma masu sha’awar sauraron makaɗan, da su gane irin tarin hikimomi da fasahohin da ke ɗamfare cikin waƙoƙin makaɗa da mawaƙa. Hakan zai fito da irin gudummawar da suke bayarwa, musamman ga harshen Hausa, ta fuskar nuna ƙwarewa da gwanintar harshe. Wannan nazari ya kaɗaita a kan salon tattsafin haliyya ne kawai. Bincike zai ba da gudummawa wajen haskawa sauran manazarta da ɗalibai yadda za su fahimci adon harshen tattasafi a cikin ire-iren waƙoƙin situdiyo na Hausa.
Title: Salon Tsattsafi a Cikin Wasu Waƙoƙin Maryam Sale Fantimoti
Description:
Makaɗan baka na Hausa kan yi amfani da hikima, da basirar da Allah ya yi musu wajen tsara maganganun, da za su ja hankalin mai sauraro ta hanyar amfani da adon harshe.
Maryam Sale Fantimoti na ɗaya daga makaɗan da Allah ya horewa wannan baiwa, da hikima da zalaƙar zance.
A wannan nazari an kalli yadda Maryam Sale Fantimoti ta yi amfani da dabaran adon harshe ta salon tsattsafi a wasu daga cikin waƙoƙinta.
An ɗora binciken bisa ra’in ƙaye (Aethtetic theory).
Dabaru da hanyoyin da ake bi wajen gudanar da wannan nazari sun haɗa da, tattaunawa da Maryam Sale Fantimoti da wasu masana.
Binciken ya gano Maryam Sale Fantimoti tana amfani da tsattsafin haliyya wanda kan haifar da raha da soyayya da farin ciki da baƙin ciki, da sauran halaye da mutane kan tsinci kan su a ciki, dukkanninsu a cikin waƙoƙin nata.
Manufar wannan takarda ita ce, jawo hankalin ɗalibai ‘yan’uwana da manazarta da ma masu sha’awar sauraron makaɗan, da su gane irin tarin hikimomi da fasahohin da ke ɗamfare cikin waƙoƙin makaɗa da mawaƙa.
Hakan zai fito da irin gudummawar da suke bayarwa, musamman ga harshen Hausa, ta fuskar nuna ƙwarewa da gwanintar harshe.
Wannan nazari ya kaɗaita a kan salon tattsafin haliyya ne kawai.
Bincike zai ba da gudummawa wajen haskawa sauran manazarta da ɗalibai yadda za su fahimci adon harshen tattasafi a cikin ire-iren waƙoƙin situdiyo na Hausa.
Related Results
Salon Jerin Sarƙe a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
Salon Jerin Sarƙe a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
Masana sun tabbatar da cewa, Salo ya ƙunshi duk wasu dabaru da hikimomin jawo hankali domin a isar da saƙo cikin harshe mai burgewa da saka karsashi da kuma jawo hankali ga mai sau...
Salon Sakaɗe a Waƙoƙin Baka na Hausa: Duba Cikin Wasu Shahararrun Waƙoƙin Mashahuran Mawaƙan Baka
Salon Sakaɗe a Waƙoƙin Baka na Hausa: Duba Cikin Wasu Shahararrun Waƙoƙin Mashahuran Mawaƙan Baka
Burin wannan bincike lalubo wani salo daga cikin salailai da mawaƙan baka ke amfani da su
wajen isar da saƙonsu ga masu sauraron su. An yi wa binciken take “Salon Sakaɗe: an ƙago s...
Zambo A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u
Zambo A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u
A kowane lokaci adabin al’uma kan fayyace yadda rayuwa da tsarin zamantakewar al’umar ke wakana ne, ta yadda ake sa rai idan an dubi adabin wannnan al’umar a iya hango hoton rayuwa...
Nazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu Waƙoƙin Siyasa na Hausa
Nazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu Waƙoƙin Siyasa na Hausa
Wannan takarda mai takenNazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu waƙoƙin siyasa na Hausa,n rubuta ta ne da niyyar fito da ire-iren hikimomi da basirar da mawallafan siyasa suke amfani da ...
Tarken Yabo da Zuga a cikin wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru
Tarken Yabo da Zuga a cikin wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru
Yabo a fagen waƙa wasu kalamai ne da ake yi domin faranta ran wanda ake yi wa waƙa. Zuga kuma ita ce ingiza ko kwarzanta wanda ake yabawa a cikin waƙa. Makaɗa Sa'idu Faru fitaccen ...
Kirari A Wasu Waƙoƙin Makaɗan Maza
Kirari A Wasu Waƙoƙin Makaɗan Maza
Wannan takarda mai suna “kirari a wasu waƙoƙin makaɗan maza” ta ƙunshi ma’anar kirari daga masana daban-daban, da rabe-raben kirari tare da fito da yanayinsa da sigoginsa da kuma y...
Turken Zuga da Yabo a Zubin Wasu Ɗiyan Waƙoƙin Alhaji Sa’idu Faru: Nazari DagaWaƙar Turakin Kano Alhaji Ahmadu
Turken Zuga da Yabo a Zubin Wasu Ɗiyan Waƙoƙin Alhaji Sa’idu Faru: Nazari DagaWaƙar Turakin Kano Alhaji Ahmadu
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin turken zuga da yabo a waƙar Turakin Kano. Don haka zuga ko yabo ɗaya ne daga cikin turakun waƙoƙin makaɗan baka na Hausa, musam...
Hannu Ba Ka Da Tsoro: Gurbin Hannu Cikin Tunanin Masu Abu “Hausawa”
Hannu Ba Ka Da Tsoro: Gurbin Hannu Cikin Tunanin Masu Abu “Hausawa”
Tunanin wannan bincike shi ne, fayyace yadda sunan hannu ya yi naso da malkashi cikin tunanin Bahaushe da ke bayyana cikin adabinsa, da al’adunsa, da harshensa. Binciken da aka yi ...

