Javascript must be enabled to continue!
Zambo A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u
View through CrossRef
A kowane lokaci adabin al’uma kan fayyace yadda rayuwa da tsarin zamantakewar al’umar ke wakana ne, ta yadda ake sa rai idan an dubi adabin wannnan al’umar a iya hango hoton rayuwarsu har kuma a tarbiyantu a dalilin hakan. Waƙa tamkar tumbin giwa ce a tsakanin sauran sassan adabi ta yadda takan ƙumshe kusan dukkan sauran sassan adabi a cikinta. Daga cikin kayan cikin waƙa kuwa, zambo ya kasance kamar shi ne maɗaciya wanda ke ɗiga ruwan da ke narkar da duk wani takaici ko huce haushi ko gugar zana da mayar da martini da mawaƙi kan yi a cikin waƙarsa, inda yakan samu sarrafa zancensa ya ɓata tare da muzanta wanda duk yake da takaicinsa ko kuma wanda yake ganin yana jayayya da shi ko kuma hamayya da wanda yake waƙewa. A cikin wannan maƙala, an yi nazarin yadda Makaɗa Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai yake sarrafa fasahar zambo a cikin waƙoƙinsa. Maƙalar ta zaƙulo wasu ɗiyan waƙoƙi daga cikin wasu waƙoƙinsa waɗanda take ganin suna ƙunshe da zambo, inda ta yi ƙoƙarin ƙwanƙwance su tare da nuna yadda makaɗin ya sarrafa fasahar tasa ya goge wanda yake da buƙata. Maƙalar ta yi sharhi dangane da yadda makaɗin ya sarrafa fasahar zambo a cikin ɗiyan waƙoƙinsa. Maƙalar ta tattara bayanan da ta sarrafa ne ta hanyar sauraron waƙoƙin makaɗin sannan ta juye su a rubuce, kana daga bisani ta zaɓo diyan da take ganin suna ɗauke da fasahar zambo tare da yi musu sharhi. Maƙalar ta zaɓo diyan waƙoƙin da ta yi amfani da su ne daga cikin waƙoƙin makaɗin a ƙalla guda biyar. A ƙarshe wannan maƙala ta tabbatar da cewa waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u cike suke da fasahar zambo.
SASPR Edu International Pvt. Ltd
Title: Zambo A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u
Description:
A kowane lokaci adabin al’uma kan fayyace yadda rayuwa da tsarin zamantakewar al’umar ke wakana ne, ta yadda ake sa rai idan an dubi adabin wannnan al’umar a iya hango hoton rayuwarsu har kuma a tarbiyantu a dalilin hakan.
Waƙa tamkar tumbin giwa ce a tsakanin sauran sassan adabi ta yadda takan ƙumshe kusan dukkan sauran sassan adabi a cikinta.
Daga cikin kayan cikin waƙa kuwa, zambo ya kasance kamar shi ne maɗaciya wanda ke ɗiga ruwan da ke narkar da duk wani takaici ko huce haushi ko gugar zana da mayar da martini da mawaƙi kan yi a cikin waƙarsa, inda yakan samu sarrafa zancensa ya ɓata tare da muzanta wanda duk yake da takaicinsa ko kuma wanda yake ganin yana jayayya da shi ko kuma hamayya da wanda yake waƙewa.
A cikin wannan maƙala, an yi nazarin yadda Makaɗa Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai yake sarrafa fasahar zambo a cikin waƙoƙinsa.
Maƙalar ta zaƙulo wasu ɗiyan waƙoƙi daga cikin wasu waƙoƙinsa waɗanda take ganin suna ƙunshe da zambo, inda ta yi ƙoƙarin ƙwanƙwance su tare da nuna yadda makaɗin ya sarrafa fasahar tasa ya goge wanda yake da buƙata.
Maƙalar ta yi sharhi dangane da yadda makaɗin ya sarrafa fasahar zambo a cikin ɗiyan waƙoƙinsa.
Maƙalar ta tattara bayanan da ta sarrafa ne ta hanyar sauraron waƙoƙin makaɗin sannan ta juye su a rubuce, kana daga bisani ta zaɓo diyan da take ganin suna ɗauke da fasahar zambo tare da yi musu sharhi.
Maƙalar ta zaɓo diyan waƙoƙin da ta yi amfani da su ne daga cikin waƙoƙin makaɗin a ƙalla guda biyar.
A ƙarshe wannan maƙala ta tabbatar da cewa waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u cike suke da fasahar zambo.
Related Results
Salon Sakaɗe a Waƙoƙin Baka na Hausa: Duba Cikin Wasu Shahararrun Waƙoƙin Mashahuran Mawaƙan Baka
Salon Sakaɗe a Waƙoƙin Baka na Hausa: Duba Cikin Wasu Shahararrun Waƙoƙin Mashahuran Mawaƙan Baka
Burin wannan bincike lalubo wani salo daga cikin salailai da mawaƙan baka ke amfani da su
wajen isar da saƙonsu ga masu sauraron su. An yi wa binciken take “Salon Sakaɗe: an ƙago s...
Salon Jerin Sarƙe a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
Salon Jerin Sarƙe a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
Masana sun tabbatar da cewa, Salo ya ƙunshi duk wasu dabaru da hikimomin jawo hankali domin a isar da saƙo cikin harshe mai burgewa da saka karsashi da kuma jawo hankali ga mai sau...
Nazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu Waƙoƙin Siyasa na Hausa
Nazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu Waƙoƙin Siyasa na Hausa
Wannan takarda mai takenNazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu waƙoƙin siyasa na Hausa,n rubuta ta ne da niyyar fito da ire-iren hikimomi da basirar da mawallafan siyasa suke amfani da ...
Tarken Yabo da Zuga a cikin wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru
Tarken Yabo da Zuga a cikin wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru
Yabo a fagen waƙa wasu kalamai ne da ake yi domin faranta ran wanda ake yi wa waƙa. Zuga kuma ita ce ingiza ko kwarzanta wanda ake yabawa a cikin waƙa. Makaɗa Sa'idu Faru fitaccen ...
Turken Zuga da Yabo a Zubin Wasu Ɗiyan Waƙoƙin Alhaji Sa’idu Faru: Nazari DagaWaƙar Turakin Kano Alhaji Ahmadu
Turken Zuga da Yabo a Zubin Wasu Ɗiyan Waƙoƙin Alhaji Sa’idu Faru: Nazari DagaWaƙar Turakin Kano Alhaji Ahmadu
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin turken zuga da yabo a waƙar Turakin Kano. Don haka zuga ko yabo ɗaya ne daga cikin turakun waƙoƙin makaɗan baka na Hausa, musam...
Salon Tsattsafi a Cikin Wasu Waƙoƙin Maryam Sale Fantimoti
Salon Tsattsafi a Cikin Wasu Waƙoƙin Maryam Sale Fantimoti
Makaɗan baka na Hausa kan yi amfani da hikima, da basirar da Allah ya yi musu wajen tsara maganganun, da za su ja hankalin mai sauraro ta hanyar amfani da adon harshe. Maryam Sale ...
Kirari A Wasu Waƙoƙin Makaɗan Maza
Kirari A Wasu Waƙoƙin Makaɗan Maza
Wannan takarda mai suna “kirari a wasu waƙoƙin makaɗan maza” ta ƙunshi ma’anar kirari daga masana daban-daban, da rabe-raben kirari tare da fito da yanayinsa da sigoginsa da kuma y...
Hamayya ko Adawa a Cikin Waƙoƙin Siyasa a Ƙasar Hausa
Hamayya ko Adawa a Cikin Waƙoƙin Siyasa a Ƙasar Hausa
Waƙa a siyasa kamar gishiri ne a cikin miya, rukuni ne kuma ginshiƙi ne babba a cikin harkokin siyasa, kusan a iya cewa, siyasa ba ta zama da ƙafafunta ba tare da waƙa ba (Usman 20...

