Search engine for discovering works of Art, research articles, and books related to Art and Culture
ShareThis
Javascript must be enabled to continue!

Salon Sakaɗe a Waƙoƙin Baka na Hausa: Duba Cikin Wasu Shahararrun Waƙoƙin Mashahuran Mawaƙan Baka

View through CrossRef
Burin wannan bincike lalubo wani salo daga cikin salailai da mawaƙan baka ke amfani da su wajen isar da saƙonsu ga masu sauraron su. An yi wa binciken take “Salon Sakaɗe: an ƙago sunan ne bisa ga tunanin magabatanmu masana ilmin waƙa. An ɗora aikin a kan mazhabar Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo na cikin Gadon Feɗe Waƙa da Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa. An yi bitar karatun fitaccen aikin salo na Farfesa Abdullahi Bayero Yahaya mai taken: Salo Asirin Waƙa. An lalubi ayyukan masana da manazarta waƙa kimani talatin (30), an saurari waƙoƙin baka da dama don tantance bagiren bincike. An fasalta aikin cikin fasaloli goma sha bakwai (17) haɗa da gabatarwa da naɗewa. Bincike ya gano babu wani masani da ya sa kai kan “Salon Sakaɗe”; kuma babu wani aiki da aka gabatar a kan kowane mataki kan “sakaɗe”. Ganin dukkanin fitattun masana adabin waƙa, ba su ambace shi ba, ba kasawa ba ce, domin ba ya daga cikin fitattun salailai da aka ambata a waƙoƙin Ingilishi da na Larabci. Don haka, na gayyato ɗiyan waƙoƙi ashirin (20) cikin shahararrun waƙoƙin shahararrun makaɗa goma (10) na Hausa. Ga bincikena na tattaro misalai fiye da hamsin (50) amma na ga suna hawa matakai shida (6) na nazarin “Sakaɗe”. An yi yunƙurin fayyace kalmar “Sakaɗe” a luga da ilmin adabi. An kakkawo dalilan bayyanarsa a waƙa da muhalinsa da amfanoninsa da masu yin sa da yadda ake sarrafa shi. Binciken ya gano cikin kowane rukunin mawaƙa ana samun bayyanar salon in ban da mawaƙan da ke waƙa su kaɗai babu ‘yan amshi waɗanda binciken ya yi wa suna kai-kaɗai-gayya. Babu wai, “Sakaɗe” salo ne mai cin gashin kansa, wanda ya cancanci a saka shi cikin salailan da za a nazari a waƙoƙin baka. Dalili kuwa shi ne, yana da rassa biyar (5) masu ma’ana a nazarin salo.
Title: Salon Sakaɗe a Waƙoƙin Baka na Hausa: Duba Cikin Wasu Shahararrun Waƙoƙin Mashahuran Mawaƙan Baka
Description:
Burin wannan bincike lalubo wani salo daga cikin salailai da mawaƙan baka ke amfani da su wajen isar da saƙonsu ga masu sauraron su.
An yi wa binciken take “Salon Sakaɗe: an ƙago sunan ne bisa ga tunanin magabatanmu masana ilmin waƙa.
An ɗora aikin a kan mazhabar Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo na cikin Gadon Feɗe Waƙa da Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa.
An yi bitar karatun fitaccen aikin salo na Farfesa Abdullahi Bayero Yahaya mai taken: Salo Asirin Waƙa.
An lalubi ayyukan masana da manazarta waƙa kimani talatin (30), an saurari waƙoƙin baka da dama don tantance bagiren bincike.
An fasalta aikin cikin fasaloli goma sha bakwai (17) haɗa da gabatarwa da naɗewa.
Bincike ya gano babu wani masani da ya sa kai kan “Salon Sakaɗe”; kuma babu wani aiki da aka gabatar a kan kowane mataki kan “sakaɗe”.
Ganin dukkanin fitattun masana adabin waƙa, ba su ambace shi ba, ba kasawa ba ce, domin ba ya daga cikin fitattun salailai da aka ambata a waƙoƙin Ingilishi da na Larabci.
Don haka, na gayyato ɗiyan waƙoƙi ashirin (20) cikin shahararrun waƙoƙin shahararrun makaɗa goma (10) na Hausa.
Ga bincikena na tattaro misalai fiye da hamsin (50) amma na ga suna hawa matakai shida (6) na nazarin “Sakaɗe”.
An yi yunƙurin fayyace kalmar “Sakaɗe” a luga da ilmin adabi.
An kakkawo dalilan bayyanarsa a waƙa da muhalinsa da amfanoninsa da masu yin sa da yadda ake sarrafa shi.
Binciken ya gano cikin kowane rukunin mawaƙa ana samun bayyanar salon in ban da mawaƙan da ke waƙa su kaɗai babu ‘yan amshi waɗanda binciken ya yi wa suna kai-kaɗai-gayya.
Babu wai, “Sakaɗe” salo ne mai cin gashin kansa, wanda ya cancanci a saka shi cikin salailan da za a nazari a waƙoƙin baka.
Dalili kuwa shi ne, yana da rassa biyar (5) masu ma’ana a nazarin salo.

Related Results

Nazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu Waƙoƙin Siyasa na Hausa
Nazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu Waƙoƙin Siyasa na Hausa
Wannan takarda mai takenNazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu waƙoƙin siyasa na Hausa,n rubuta ta ne da niyyar fito da ire-iren hikimomi da basirar da mawallafan siyasa suke amfani da ...
Salon Tsattsafi a Cikin Wasu Waƙoƙin Maryam Sale Fantimoti
Salon Tsattsafi a Cikin Wasu Waƙoƙin Maryam Sale Fantimoti
Makaɗan baka na Hausa kan yi amfani da hikima, da basirar da Allah ya yi musu wajen tsara maganganun, da za su ja hankalin mai sauraro ta hanyar amfani da adon harshe. Maryam Sale ...
Salon Jerin Sarƙe a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
Salon Jerin Sarƙe a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
Masana sun tabbatar da cewa, Salo ya ƙunshi duk wasu dabaru da hikimomin jawo hankali domin a isar da saƙo cikin harshe mai burgewa da saka karsashi da kuma jawo hankali ga mai sau...
Zambo A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u
Zambo A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u
A kowane lokaci adabin al’uma kan fayyace yadda rayuwa da tsarin zamantakewar al’umar ke wakana ne, ta yadda ake sa rai idan an dubi adabin wannnan al’umar a iya hango hoton rayuwa...
Tarken Yabo da Zuga a cikin wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru
Tarken Yabo da Zuga a cikin wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru
Yabo a fagen waƙa wasu kalamai ne da ake yi domin faranta ran wanda ake yi wa waƙa. Zuga kuma ita ce ingiza ko kwarzanta wanda ake yabawa a cikin waƙa. Makaɗa Sa'idu Faru fitaccen ...
Salon Shillo a Bakin Makaɗan Baka na Hausa
Salon Shillo a Bakin Makaɗan Baka na Hausa
An gabatar da wannan tsokaci domin shiga sahun marubuta maƙalu domin karrama Farfesa Abdullahi BayeroYahya. Manufar wannan tsokaci shi ne a yi nazarin wani salo wanda masana suka k...
Hausa
Hausa
With an estimated population of up to 50 million, Hausa make up one of the largest people groups practicing Islam. Despite settlement of today’s Hausaland in the central Sudan by t...
Nazarin Tsarin Sauti a Wasu Zaurance Na Hausa
Nazarin Tsarin Sauti a Wasu Zaurance Na Hausa
Zaurance yana ɗaya daga cikin azancin da harshen Hausa ya yi fice da su wanda matasa musamman mata suke amfani da shi wajen sakaya zance ta hanyar sauya masa wasu fitattun kamannin...

Back to Top