Javascript must be enabled to continue!
Kirari A Wasu Waƙoƙin Makaɗan Maza
View through CrossRef
Wannan takarda mai suna “kirari a wasu waƙoƙin makaɗan maza” ta ƙunshi ma’anar kirari daga masana daban-daban, da rabe-raben kirari tare da fito da yanayinsa da sigoginsa da kuma yadda yake yin naso a cikin wasu waƙoƙin makaɗan maza. A yayin rubuta takardar an bi waɗannan watau bibiyar wasu daga cikin bugaggun littattafai waɗanda masana suka rubuta domin fito da misalai. Haka kuma a takardar an kawo wasu sigogin kirari guda biyar (5) da makaɗan maza kan yi amfani da su wajen gina waƙoƙinsu na kirari, waɗanda suka haɗa da kirari da sigar yin zuga da kirari ta sigar nuna jarumta, da kirari ta sigar nuna bajinta da kirari ta sigar siffantawa da kuma kirari ta sigar yin yabo. Daga ƙarshe an kawo kammalawa da manazarta.
SASPR Edu International Pvt. Ltd
Title: Kirari A Wasu Waƙoƙin Makaɗan Maza
Description:
Wannan takarda mai suna “kirari a wasu waƙoƙin makaɗan maza” ta ƙunshi ma’anar kirari daga masana daban-daban, da rabe-raben kirari tare da fito da yanayinsa da sigoginsa da kuma yadda yake yin naso a cikin wasu waƙoƙin makaɗan maza.
A yayin rubuta takardar an bi waɗannan watau bibiyar wasu daga cikin bugaggun littattafai waɗanda masana suka rubuta domin fito da misalai.
Haka kuma a takardar an kawo wasu sigogin kirari guda biyar (5) da makaɗan maza kan yi amfani da su wajen gina waƙoƙinsu na kirari, waɗanda suka haɗa da kirari da sigar yin zuga da kirari ta sigar nuna jarumta, da kirari ta sigar nuna bajinta da kirari ta sigar siffantawa da kuma kirari ta sigar yin yabo.
Daga ƙarshe an kawo kammalawa da manazarta.
Related Results
Salon Jerin Sarƙe a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
Salon Jerin Sarƙe a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
Masana sun tabbatar da cewa, Salo ya ƙunshi duk wasu dabaru da hikimomin jawo hankali domin a isar da saƙo cikin harshe mai burgewa da saka karsashi da kuma jawo hankali ga mai sau...
Nazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu Waƙoƙin Siyasa na Hausa
Nazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu Waƙoƙin Siyasa na Hausa
Wannan takarda mai takenNazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu waƙoƙin siyasa na Hausa,n rubuta ta ne da niyyar fito da ire-iren hikimomi da basirar da mawallafan siyasa suke amfani da ...
Salon Tsattsafi a Cikin Wasu Waƙoƙin Maryam Sale Fantimoti
Salon Tsattsafi a Cikin Wasu Waƙoƙin Maryam Sale Fantimoti
Makaɗan baka na Hausa kan yi amfani da hikima, da basirar da Allah ya yi musu wajen tsara maganganun, da za su ja hankalin mai sauraro ta hanyar amfani da adon harshe. Maryam Sale ...
Tarken Yabo da Zuga a cikin wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru
Tarken Yabo da Zuga a cikin wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru
Yabo a fagen waƙa wasu kalamai ne da ake yi domin faranta ran wanda ake yi wa waƙa. Zuga kuma ita ce ingiza ko kwarzanta wanda ake yabawa a cikin waƙa. Makaɗa Sa'idu Faru fitaccen ...
Turken Zuga da Yabo a Zubin Wasu Ɗiyan Waƙoƙin Alhaji Sa’idu Faru: Nazari DagaWaƙar Turakin Kano Alhaji Ahmadu
Turken Zuga da Yabo a Zubin Wasu Ɗiyan Waƙoƙin Alhaji Sa’idu Faru: Nazari DagaWaƙar Turakin Kano Alhaji Ahmadu
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin turken zuga da yabo a waƙar Turakin Kano. Don haka zuga ko yabo ɗaya ne daga cikin turakun waƙoƙin makaɗan baka na Hausa, musam...
Zambo A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u
Zambo A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u
A kowane lokaci adabin al’uma kan fayyace yadda rayuwa da tsarin zamantakewar al’umar ke wakana ne, ta yadda ake sa rai idan an dubi adabin wannnan al’umar a iya hango hoton rayuwa...
Wasu Ƙananan Tubalan Turken Yabon Mata a Zubin Wasu Waƙoƙin Shata
Wasu Ƙananan Tubalan Turken Yabon Mata a Zubin Wasu Waƙoƙin Shata
Yabo na cikin manyan turakun da makaɗan baka suka fi yawaita yin waƙoƙi na baka a kan sa. Kusan shi ne ma fitaccen turken waƙoƙin baka na Hausa domin mafi yawan waƙoƙin manufofinsu...
Salon Sakaɗe a Waƙoƙin Baka na Hausa: Duba Cikin Wasu Shahararrun Waƙoƙin Mashahuran Mawaƙan Baka
Salon Sakaɗe a Waƙoƙin Baka na Hausa: Duba Cikin Wasu Shahararrun Waƙoƙin Mashahuran Mawaƙan Baka
Burin wannan bincike lalubo wani salo daga cikin salailai da mawaƙan baka ke amfani da su
wajen isar da saƙonsu ga masu sauraron su. An yi wa binciken take “Salon Sakaɗe: an ƙago s...

