Search engine for discovering works of Art, research articles, and books related to Art and Culture
ShareThis
Javascript must be enabled to continue!

Bokanci Da Tsibbu a Littafin Komai Nisan Dare

View through CrossRef
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin ayyakun bokanci da tsibbu a tsarin zamantakewar Hausawa daga littafin Komai Nisan Dare. Haka kuma, an yi amfani da hanyar nazarin ƙagaggun labarai, wato Mukhtar (2004). Haka kuma, an tsakuro misalan da aka yi sharhin su a wannan nazari daga littafin Kome Nisan Dare, wato Bambale (2009). Har ila yau, a sakamakon wannan nazari an fahimci, marubuta ƙagaggun labarai sukan lura da yanayin zamantakewar aure wajen rubutunsu ta hanyar fito da wasu halaye da ɗabi’u da suka faru, musamman a zamantakewar iri ta kishi. Hakazalika, an lura a wannan littafin an nuna yanayin aikin bokaye da hanyoyi da suke bi wajen amfani Aljannu da kuma yadda ayyukan nasu yawanci ƙarya ce. Sannan kuma, an nuna yanayin aikin Malaman tsibbu ta hanyar yi addu’o’i ta hanyar neman taimakon Allah don samun biyan buƙata. Har wa yau, an gano tsarin zamantakewar aure gaskiya da haƙuri su ne mafita ba zuwa wajen bokaye ba. Saboda komai daɗewa asiri zai tonu, wato za a girbi abin da aka shuka. Kamar yadda Binta ta nuna gaskiya da haƙuri ta yi nasara da kuma fito da yadda Tsigarallahu ta bi hanyar bokaye a ƙarshe ta ji kunya, wato, aka saketa kuma daga baya ta haukace. Har ila yau, an fahimci, mutum ya yi haƙuri ya daure ya taimaki wanda ya cutar da shi lokacin da ya ga ya shiga wani mawuyacin hali, yakan ƙara wa mutum daraja da kwarjini a idon wannan mutum. Sannan kuma, shi da ya yi cutar, ya ga kuma an taimaki shi a lokaci da babu wanda zai taimaka masa yakan ji kunya kuma ya yi danasanin abin da ya aikata a baya, kamar yadda ta faru tsakanin Saluhu da Tsigarallahu.
Title: Bokanci Da Tsibbu a Littafin Komai Nisan Dare
Description:
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin ayyakun bokanci da tsibbu a tsarin zamantakewar Hausawa daga littafin Komai Nisan Dare.
Haka kuma, an yi amfani da hanyar nazarin ƙagaggun labarai, wato Mukhtar (2004).
Haka kuma, an tsakuro misalan da aka yi sharhin su a wannan nazari daga littafin Kome Nisan Dare, wato Bambale (2009).
Har ila yau, a sakamakon wannan nazari an fahimci, marubuta ƙagaggun labarai sukan lura da yanayin zamantakewar aure wajen rubutunsu ta hanyar fito da wasu halaye da ɗabi’u da suka faru, musamman a zamantakewar iri ta kishi.
Hakazalika, an lura a wannan littafin an nuna yanayin aikin bokaye da hanyoyi da suke bi wajen amfani Aljannu da kuma yadda ayyukan nasu yawanci ƙarya ce.
Sannan kuma, an nuna yanayin aikin Malaman tsibbu ta hanyar yi addu’o’i ta hanyar neman taimakon Allah don samun biyan buƙata.
Har wa yau, an gano tsarin zamantakewar aure gaskiya da haƙuri su ne mafita ba zuwa wajen bokaye ba.
Saboda komai daɗewa asiri zai tonu, wato za a girbi abin da aka shuka.
Kamar yadda Binta ta nuna gaskiya da haƙuri ta yi nasara da kuma fito da yadda Tsigarallahu ta bi hanyar bokaye a ƙarshe ta ji kunya, wato, aka saketa kuma daga baya ta haukace.
Har ila yau, an fahimci, mutum ya yi haƙuri ya daure ya taimaki wanda ya cutar da shi lokacin da ya ga ya shiga wani mawuyacin hali, yakan ƙara wa mutum daraja da kwarjini a idon wannan mutum.
Sannan kuma, shi da ya yi cutar, ya ga kuma an taimaki shi a lokaci da babu wanda zai taimaka masa yakan ji kunya kuma ya yi danasanin abin da ya aikata a baya, kamar yadda ta faru tsakanin Saluhu da Tsigarallahu.

Related Results

BENTUK DAN MAKNA RAGAM HIAS NISAN PADA MAKAM MASYARAKAT DESA HENDEA
BENTUK DAN MAKNA RAGAM HIAS NISAN PADA MAKAM MASYARAKAT DESA HENDEA
Nisan kubur merupakan tanda tentang adanya sebuah peradaban dan kepercayaan yang dimiliki oleh masyarakat pendukungnya. Begitu pula nisan Mayasa yang dimiliki masyarakat Desa Hende...
Salo a Littafin Amon ‘Yanci na Halima Ahmad Matazu
Salo a Littafin Amon ‘Yanci na Halima Ahmad Matazu
Fagen nazarin salo, fage ne mai faxi wanda yake da buqatar a ci gaba da nazarta domin fito da hikimomi da zalaqar harshe da Allah ya albarkaci fasihai da marubuta na Hausa. Duk da ...
MAKAM KUNO BELANDA DI KELURAHAN KANDAI KOTA KENDARI PROVINSI SULAWESI TENGGARA
MAKAM KUNO BELANDA DI KELURAHAN KANDAI KOTA KENDARI PROVINSI SULAWESI TENGGARA
Penelitian ini mengidentifikasi dan menjelaskan bentuk serta variasi nisan dan jirat (kijing) makam Belanda di Kelurahan Kandai Kota Kendari. Penelitian ini termasuk penelitian kua...
Kudüs’te Görünür Olma Siyaseti: Osmanlı Nişan Taltifleri (1872-1917)
Kudüs’te Görünür Olma Siyaseti: Osmanlı Nişan Taltifleri (1872-1917)
19. yy. diplomasisinin taltif araçlarından biri olarak kullanılan nişanlar, tüm dünyada olduğu gibi Osmanlı devleti tarafından da yaygın bir şekilde kullanıldı. Modern dönemde, dip...
Estimation of Fetal Weight by Clinical Method &  Ultrasonography & It's Correlation with Actual Birth Weight In Term Pregnancy
Estimation of Fetal Weight by Clinical Method &  Ultrasonography & It's Correlation with Actual Birth Weight In Term Pregnancy
Background: Accurate estimation of fetal weight (EFW) is a crucial component of prenatal care, guiding decisions regarding delivery timing, mode of delivery, and neonatal managemen...

Back to Top