Javascript must be enabled to continue!
Nazarin Rikiɗar Wasu Sautukan Harshen Ngizim Zuwa Hausa
View through CrossRef
A duk lokacin da aka samu wata cuɗanya ta mu’amala tsakanin harsuna mabambanta guda biyu, akan samu harshe mafi tasiri a tsakaninsu. Irin wannan dangantaka ta tsakanin harsuna, ita takan sa harshe mafi tasiri ya yi naso har ya kawo wasu sauye-sauye a wani ɓangare na harshe abokin mu’amalarsa mai ƙarancin ƙarfin tasiri. Harshen Hausa da na Ngizim, harsuna ne da suke da ƙullalliyar alaƙa ta asali ɗaya da kuma ta mu’amala bisa tsarin zamantakewa. Manufar wannan bincike ita ce, nazartar irin rikiɗar da wasu sautukan Ngizim sukan yi ta hanyar narkewar furucinsu na asali zuwa wasu na daban a Hausa. Dangane da hanyoyin gudanar da binciken, an yi amfani da dabarar tatsar bayanai daga ‘yan asalin harshen Ngizim ta hanyar sauraron maganganunsu a muhallai daban-daban da kuma karantawa daga wallafaffun littattafai da takardu na masana domin tantancewa da ma kafa hujja a kan bayannan da aka tatsa. Haka nan, Ra’in Tsarin Sauti Ɗan Tsirau (Theory of Generative Phonology) na Chomsky da Halle, (1968) da kuma Ra’in Cuɗanya (Contact Theory) na Uriel Weinreich (1953) su aka yi amfani da su a matsayin ra’in da aka ɗora binciken a kai. Bugu da ƙari, binciken ya gano cewa, wasu keɓaɓɓun sautuka a harshen Ngizim kamar /ə/ da /dl/ da /tl/ da kuma /zh/ suna rikiɗa zuwa wasu sautuka na harshen Hausa sakamakon ƙarfin tasirin da harshen na Hausa ya yi a kan na Ngizim.
SASPR Edu International Pvt. Ltd
Title: Nazarin Rikiɗar Wasu Sautukan Harshen Ngizim Zuwa Hausa
Description:
A duk lokacin da aka samu wata cuɗanya ta mu’amala tsakanin harsuna mabambanta guda biyu, akan samu harshe mafi tasiri a tsakaninsu.
Irin wannan dangantaka ta tsakanin harsuna, ita takan sa harshe mafi tasiri ya yi naso har ya kawo wasu sauye-sauye a wani ɓangare na harshe abokin mu’amalarsa mai ƙarancin ƙarfin tasiri.
Harshen Hausa da na Ngizim, harsuna ne da suke da ƙullalliyar alaƙa ta asali ɗaya da kuma ta mu’amala bisa tsarin zamantakewa.
Manufar wannan bincike ita ce, nazartar irin rikiɗar da wasu sautukan Ngizim sukan yi ta hanyar narkewar furucinsu na asali zuwa wasu na daban a Hausa.
Dangane da hanyoyin gudanar da binciken, an yi amfani da dabarar tatsar bayanai daga ‘yan asalin harshen Ngizim ta hanyar sauraron maganganunsu a muhallai daban-daban da kuma karantawa daga wallafaffun littattafai da takardu na masana domin tantancewa da ma kafa hujja a kan bayannan da aka tatsa.
Haka nan, Ra’in Tsarin Sauti Ɗan Tsirau (Theory of Generative Phonology) na Chomsky da Halle, (1968) da kuma Ra’in Cuɗanya (Contact Theory) na Uriel Weinreich (1953) su aka yi amfani da su a matsayin ra’in da aka ɗora binciken a kai.
Bugu da ƙari, binciken ya gano cewa, wasu keɓaɓɓun sautuka a harshen Ngizim kamar /ə/ da /dl/ da /tl/ da kuma /zh/ suna rikiɗa zuwa wasu sautuka na harshen Hausa sakamakon ƙarfin tasirin da harshen na Hausa ya yi a kan na Ngizim.
Related Results
Nazarin Tsarin Sauti a Wasu Zaurance Na Hausa
Nazarin Tsarin Sauti a Wasu Zaurance Na Hausa
Zaurance yana ɗaya daga cikin azancin da harshen Hausa ya yi fice da su wanda matasa musamman mata suke amfani da shi wajen sakaya zance ta hanyar sauya masa wasu fitattun kamannin...
Nazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu Waƙoƙin Siyasa na Hausa
Nazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu Waƙoƙin Siyasa na Hausa
Wannan takarda mai takenNazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu waƙoƙin siyasa na Hausa,n rubuta ta ne da niyyar fito da ire-iren hikimomi da basirar da mawallafan siyasa suke amfani da ...
Hausa Political Music and Political Engagements on Social Media during Nigeria’s 2023 General Elections
Hausa Political Music and Political Engagements on Social Media during Nigeria’s 2023 General Elections
The use of Hausa political music has become a key feature during electioneering campaigns in
northern parts of Nigeria. This paper examines how Hausa political music were used for...
Salon Tsattsafi a Cikin Wasu Waƙoƙin Maryam Sale Fantimoti
Salon Tsattsafi a Cikin Wasu Waƙoƙin Maryam Sale Fantimoti
Makaɗan baka na Hausa kan yi amfani da hikima, da basirar da Allah ya yi musu wajen tsara maganganun, da za su ja hankalin mai sauraro ta hanyar amfani da adon harshe. Maryam Sale ...
Nazarin Hanyar Sadarwa Ta Girafiti A Karin Maganar Hausa
Nazarin Hanyar Sadarwa Ta Girafiti A Karin Maganar Hausa
Hanyoyin sadarwa domin isar da saƙonni sun kasu kasha daban-daban musamman idan aka yi la’akari da yanayin yadda akan sarrafa hanyoyin da kuma yanayin waɗanda akan isar wa saƙonnin...
Sarrafa Harshen Mawallafiya a Matsayin Dabarar Bayar da Labari a Wasu Ƙagaggun Rubutattun Labaran Hausa na Balaraba Ramat Yakubu
Sarrafa Harshen Mawallafiya a Matsayin Dabarar Bayar da Labari a Wasu Ƙagaggun Rubutattun Labaran Hausa na Balaraba Ramat Yakubu
Wannan aiki yana ƙunshe da bayanai dangane da yadda mawallafiya ta yi amfani da dabarar sarrafa harshe domin ta yaɗa wasu al’adun Hausawa da kuma na wasu al’ummomin da ba Hausawa b...

